✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sibil Difens Ta Kama Masana’antar Gurbataccen Man Dizel A Gombe

Hukumar NSCDC ta kama wata masana'antar hada gurbataccen man Dizel a Jihar Gombe.

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta kama wata masana’antar hada gurbataccen man Dizel a Jihar Gombe.

Kwamandan hukumar a jihar Gombe Muhammad Bello Mu’azu, ya ce, sun gano masana’antar ce a unguwar Federal Low Cost bayan wani rahoton sirri da suka samu daga mutanen gari.

Mu’azu, ya ce an kafa masana’antar ce ba bisa ka’ida ba lamarin da ya sa suka hada guiwa da Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki (SON) suka rufe ta.

Ya ce bugu da kari gina wajen a cikin al’umma yana gurbata muhalli, ga warin sinadarin da ke cutar da makwabta kuma babu rajista kowacce iri.

A nasu bangaren hukumar SON ta bakin Mukaddashin Kwanturola na jihar Abbas Adamu, ya bayyana cewa duk da cewa gwamnatin Najeriya na goyon bayan an Samar da kamfanoni na cikin gida amma ba ta ce a gina su ba bisa tsari da bin ka’ida ba.

Abbas, ya ce, “Za mu dauki samfuri mu kai dakin bincike mu gwada ingancinsa; nan ba da dadewa ba za mu sanar da jama’a sakamakon gwajin domin daukar mataki na gaba; amma daga yanzu mun rufe masana’antar har zuwa wani lokaci,” in ji SON.

Mamallakin masana’antar, Abubakar Aliyu, ya ce shi ya kafa ta ne a jikin gidansa kuma kimanin makonni uku da suka wuce kuma bai san akwai hukumar SON ba, amma ya so ya yi rajista da ma’aikatar muhalli saboda yadda aikin nasa yake gurbata muhalli.

Aliyu, yace shi Dan kasuwa ne Mai fadi tashi, da bai yadda da zaman banza ba shi yasa ya kirkiro wannan Masana’antar da take Samar da man Dizel.

Ya ce sinadaran da yake hadawa na samar da man dizel din su ne lalataccen bakin mai da ledodi da bawon doya da gawayi da wasu sinadarai.

Wasu ’yan kasuwa masu sayen man dizel din daga wajensa, Alhaji Iliya Mai kananzir da Abdurrashid Alhaji Sani cewa suka yi, suna saya daga wajensa ne saboda sun dauka daga Warri yake kawowa Ba su sannan a nan Gombe yake hadawa ba.

Sun ce yadda suke sayen wanda ake kawowa daga Matatar Mai ta Warri haka suke sayen sa. Amma shi wanda yake kawo musu din akwai banbancin kyau da kauri, wanda har masu injunan nika a kauyuka sun gano idan ba wannan din ba basa sayen wani.

“Tunda muka fara Sayar da shi ba Wanda ya taba saya yaje ya dawo yace mana bai da kyau kowa yaba shi yake yi shi yasa ma masu injunan Nika suka dawo sai shi suke saya.