✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sirri da ƙalubalen da ke cikin sana’ar makara

Wasu suna cewa musu sana'ar hada makara ’yan ina-da-mutuwa ko marasa tausayi.

Sana’ar yin makara ko tukurwa sana’a ce da mutane da dama ke kyama. Sai dai abin da ba a sani ba shi ne, sana’a ce mai muhimmncin gaske da wasu mutane ke yin ta kusan shekara 200 da suka gabata a Kasar Hausa, kamar yadda jaridar Aminiya ta gano.

Duk da zafin rana da ake fama da shi da kuma matsin tattalin arziki, mutane ne birjik kowa na neman na rufa wa kai asiri.

A irin wannan yanayi ne a Unguwar Tudun Nufawa da ke cikin birnin Kano, a kan hanyar da za ta sada ka da fitacciyar kasuwa nan ta Kurmi wakilin Aminiya ya iske wasu jajirtattun mutane na ta aikinsu.

Suna ta shiryawa da jerawa da kuma tamke kwangwala, wato dai suna sana’anta makara.

Wani abin sha’awa shi ne mun same su cikin annashuwa da farin ciki suna aiki suna ta hira.

Kuma ganin nasu a wannan yanayi zai tabbatar maka da cewa wannan sana’a ba wai abar kyama ba ce kamar yadda wasu ke gani ko tunani.

Wakilin Aminiya ya yi karo da daya daga cikin masu wannan sana’a ta makara mai suna Alhaji Sani Hassaini mai shekara 65, wanda ya samu karatun zamani, domin yana da takardar diploma a darussan Hausa da Larabci da Nazarin Addinin Musulunci.

Tsohon malamin makaranta ne da ya yi ritaya yana karbar fansho. Ya shaida wa Aminiya cewa, yana alfahari da wannan sana’a tun yana karamin yaro.

A wannan al’umma tamu dai ana yi wa masu wannan sana’a wani gani-gani.

Wasu su ce musu ’yan ina-da-mutuwa ko marasa tausayi. Shi ya sa ma ba kowa ne ke iya yin wannan sana’a ba. “Wannan sana’a ce ta gida,” in ji shi, yana mai cewa tashi na yi a gidanmu na ga ana yi.

“Za ka iya cewa gadarta na yi domin haka na tashi na ga ana wannan sana’a ta yin makara.

“Haka ake ta juyawa iyaye da kakanni. Kakannin kakanni mu ne suka fara ta kusan shekara dari biyu da suka gabata.

“Fatanmu shi ne mu ma mu gadar wa ’yan baya,” ya shaida wa Aminiya haka fuskarsa cike da annashawa, har ana iya ganin hakorinsa na Makka.

Lokacin da jaridar Aminiya ta ziyarci wajan abin da za ka bayyana shi da ‘Masana’antar Makara,’ wadda ake gudanarwa a kofar Gidan Sarkin Tukurwa, mun iske masu sana’ar na ta aiki cikin farin ciki da hadin kai.

A wannan sana’a da ake wa kallon hadarin kaji Malam Husaini na ganin cewa yanzu jama’a sun fara sauya tunaninsu a kanta, domin ana daukar sana’ar tamkar ta kafinta ce.

Kuma ya kara da cewa hakan ya kamata domin guje wa yi musu yin ta kallo na daban.

Masu wannan sana’a suna amfani da itaciyar tukurwa ko kwagwala da ake kira da Ingilishi da bamboo. Suna sarrafa ta ta hanyoyi daban-daban da kayan aiki na gida.

Ana yin makara ce daidai bukata; wata ta masu kiba da ta sirara da ta dogaye da ta gajeru da kuma ta yara kanana.

Mafi yawan masu sayen kayayyakin na gida ne, amma kamar yadda Hussaini ya ce, mutane daga Jamhuriyyar Nijar da Kamaru da Chadi duk suna zuwa su saya su tafi da su kasashensu domin amfani da su.

Makera sun yi yunkurin kera makara ta karfe wadda har ta samu karbuwa, amma sai batagari su rika bi masallatai cikin dare suna sacewa.

“Wannan ya sa dole aka ga cewa dai makarar kwangwala ita ce daidai. Don haka dole aka hakura ake amfani da ita,” in ji shi.

Baya ga makara, suna kuma sana’anta tsani da kwabed da sauran kayan amfanin gida gami da wata kujera ta musamman da ake kira karaga domin sarakuna da attajirai da manyan malamai.

Shi ya sa kowace shekara Sarkin Tukurwa yakan kera karaga guda biyu da ake kai wa Sarkin Kano.

Shi Kuma Sarki sai ya ba da kyautar riga ta alfarma ga Sarkin Tukurwa domin nuna jin dadinsa da wannan kyauta.

Malam Tasi’u Hassan shi ne Sarkin Tukurwa na yanzu kuma na shida a zuriyar gidan, ya shaida wa Aminiya cewa suna da kyakkyawar alaka a tsakanin gidansu da Masarautar Kano, wadda take kallonsu da kima da daraja.

Malam Tasi’u Husaini ya ce su a wajensu, sana’ar makara aiki ne mai zaman kansa, domin da ita suke rike iyalansu.

“Ni ina daukar wannan sana’a a matsayin aiki. Ina jin dadin yin ta kuma tana biya min bukatuna.

“Shekara da shekaru haka muke. Magidanci ne ni da ’ya’ya shida, da ita nake kula da su,” in ji shi.

Sai dai ya ce a kowane kasuwanci, akwai lokacin da ake hada-hada akwai lokacin da babu laifi sannan akwai lokacin da ake ji a jiki.

Malam Tasi’u ya ce abin da yake damunsa shi ne duk da samun yawaitar masallatai a birane da kauyuka ba a sayen makara a sa a ciki.

Sai dai in an yi mutuwa a zo tsofaffin masallatai domin neman aron makara domin kai mamaci da ita.

“Makara wata aba ce da ake saya lokacin bukatarta. In aka saya tana iya kaiwa shekara 50 ba ta lalace ba gwargwadon irin kyan kirarrta,” in ji shi.

Malam Tasi’u ya nuna damuwa kan yadda da daman matasa ba sa tunanin su shiga wannan sana’a “Sun gwammace su tafi wasu harkokin kasuwanci a kasuwanni ko aikin albashi,” in ji shi.

Ya bukaci gwamnati da masu hannu da shuni a cikin al’umma su rika sayen makarar suna kaiwa masallatan khamsu salawati da na Juma’a a ciki da wajen Kano a wani mataki na karfafa musu gwiwa. In aka yi haka, to matasa da dama za su zo a dama da su domin harkar za ta kawo kudi.

Ya shaida wa Aminiya cewa gwamnati za ta iya shigowa harkar tasu ta hanyar samar musu da wuri na dindindin.

“A da muna wurin da muke wannan sana’a a inda yanzu filin wasa na Sani Abacha da ke Kano yake. Sai dai mun rasa shi sakamakon bunkasar Kano.

“Haka muna da wani a Gwauron Dutse inda yanzu aka gina Masallacin Jumu’a na Khalifa Isyaka Rabi’u da ke Karamar Hukumar Dala a Birnin Kano, wanda muka samu daga Masarautar Kano, shi ma mun rasa shi,” in ji shi.

Malam Tasi’u Husaini ya kara da cewa samun wajen sana’a na dindindin zai kawo bunkasar sana’ar tasu, domin zai fito da su duniya ta gan su.