✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto mutum 9 da aka sace a Kaduna

Sojojin sun yi artabu da maharan kafin daga bisani su ceto wadanda aka sace.

Dakarun Runduna ta Daya ta Sojin Kasa ta Najeriya sun ceto mutane tara da aka sace tare da kwato makamai a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Laftana-Kanar Musa Yahaya, ya ce sojojin suna sintiri a yankin Kanzaure ne suka samu rahoton garkuwa da wasu mutane 11 a kauyukan Anguwan Maharba da Dandami.

Yahaya ya ce sojojin sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna a mashigarsu, inda suka yi dauki ba dadi, suka kubutar da mutanen a ranar 8 ga watan Disamba, 2023.

“’Yan bindigar sun tsere bayan barin wutar inda sojojin suka ceto mutane tara, amma  ’yan bindigar sun kashe biyu daga cikin wadanda suka sacen kafin isowar sojojin.”

A cewarsa, an samu kwato bindiga kirar AK47 guda daya da kuma bindiga kirar gida daya daga hannun ’yan bindigar.

Yahaya ya ce babban hafsan rundunar kuma kwamandan runduna  Operation Whirl Punch, Manjo-Janar Valentine Okoro, ya yaba wa sojojin sannan ya umarce su da kada su yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da tsaron ’yan kasa a yankin.

Okoro ya bukaci jama’a da su rika bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro sahihan bayanan sirri don magance matsalar rashin tsaro a yankin.