‘Sojoji sun kashe masu zanga-zanga 13 a Chadi’ | Aminiya

‘Sojoji sun kashe masu zanga-zanga 13 a Chadi’

Wasu Sojojin Chadi
Wasu Sojojin Chadi
    Ishaq Isma’il Musa

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch ta ce dakarun soji a Gabashin kasar Chadi sun kashe masu zanga-zanga akalla 13.

Kungiyar ta ce daga cikin wadanda dakarun sojin suka kashe har da wani yaro dan shekara 12, wadanda ke zanga-zangar lumana a daidai lokacin da ake fama da rikicin kabilanci a yankinsu.

Jama’a a garin Abeche sun gudanar da zanga-zanga ce domin nuna adawa da shirin nada wani jami’in da ya fito daga kabilar Larabawa a wani wuri da aka kebe domin sarkin al’ummar yankin Ouaddaien.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa tare da takwararta ta kasar Chadi, kungiyar kare hakkin Bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce a ranar 24 ga watan Janairu, sojoji suka tarwatsa dubban masu zanga-zangar, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu akalla 40.

Kwana guda bayan tashin hankalin ne kuma, a wajen jana’izar wadanda suka mutu, sojoji suka bude wuta kan mutane inda suka kashe karin mutane 10 tare da jikkata wasu akalla 40.

Kungiyoyin na kare hakkin dan Adam sun kara da cewar a jumlace jami’an tsaron Chadi sun kama mutane 212 kuma kuma suka tsare su har na tsawon kwanaki biyar cikin azabtarwa kafin sakinsu.

Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito cewa wannan rahoto dai ya dogara ne kan hirar da masu fafutukar kare hakkin suka yi da wani adadi na shaidu, likitoci biyu da wakilan kungiyoyin fararen hula, da kuma bidiyo da hotuna, da suka tattara.

Sai dai ministan sadarwa Abderaman Koulamallah, kuma kakakin gwamnatin mulkin sojan Chadi ya musanta cewar sojoji sun bude wuta kan fararen hula, illa kawai kokarin da suka yi don kwantar da tarzomar da masu zanga-zanga suka fara.

Minitsan ya kuma ce kamata yayi a jira sakamakon binciken da gwamnati za ta fitar.