✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kwato makamai da babura a hannun ‘yan bindiga a Kaduna

Sojojin sun yi artabu da maharan inda suka raraka su sannan suka kwato makamansu.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kwato makamai da babura daga hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.

Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Sojoji, Laftanar-Kanar Musa Yahaya ne, ya sanar cewa hakan na daga cikin kokarin dakarun na kawar da ’yan bindiga daga dazukan Kaduna.

Yahaya, ya ce sojojin suna aiki da sahihan bayanai a yankin Dogon Dawa zuwa Damari a Karamar Hukumar Igabi, inda suka yi wa maharan kwanton bauna a ranar Talata.

Ya bayyana cewa a yayin artabun, ’yan bindigar sun gudu sakamakon ruwan wutar da sojojin suka yi musu.

“Sojojin sun fatattake su, sun kuma kwato bindiga AK-47 guda daya da harsasai.

“Kazalika, sojojin da aka tura Kwanar Mutuwa a Birnin Gwari sun samu bayanan sirri kan ’yan bindiga.

“Dakarun sun yi saurin kai dauki yankin kuma nan take suka fatattake su,” in ji Yahaya.