✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun sake cafke ’yan Darul Salam 290 a Arewa

A jiya Laraba dakarun sojin Najeriya sun sake cafke wasu ’yan kungiyar tayar da kayar baya ta Darul Salam guda 290 a sassan jihohin Kogi…

A jiya Laraba dakarun sojin Najeriya sun sake cafke wasu ’yan kungiyar tayar da kayar baya ta Darul Salam guda 290 a sassan jihohin Kogi da Nasarawa.

Babban jami’in harkokin sadarwa na Rundunar Tsaro, Manjo Janar John Enenche, shi ne ya sanar da hakan a Abuja yayin taron manema labarai na mako-mako da ake gudanarwa kan al’amuran da suka shafi aikin dakaru a fadin kasar.

Ya ce wannan adadi doriya ne a kan ’yan kungiyar fiye da 400 da suka suka ce sun mika wuya kwanan nan a Karamar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa wanda yawancin su mata ne da yara kanana.

Manjo Janar Enenche ya ce a yayin sintiri da rundunar sojin ta ke gudanarwa ta gano wata cibiya da kungiyar take kera abubuwan fashewa da rokoki da gurneti.

A baya-bayan nan ne mazauna yankin Uttu a Jihar Nasarawa suka ce kungiyar Darul Salam ta jima mayakanta na kai musu hari, kuma sun hallaka mutane da dama da kuma kona garuruwan da ke yankin, ciki har da garin Dausu.