✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda a Nasarawa

A wani yanayi mai kama da ana maganin kafa kai na dada kumbura, al’ummar wani gari da aka tarwatsa a shekarar 2009 a Karamar Hukumar…

A wani yanayi mai kama da ana maganin kafa kai na dada kumbura, al’ummar wani gari da aka tarwatsa a shekarar 2009 a Karamar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa bisa zargin kasancewa na ‘yan ta’adda sun sake bulla.

An gano mutanen ne ranar Laraba yayin wani sintiri na rundunar Operation Whirl Stroke bayan wani rahoton sirri a garin mai nisan kimanin kilomita 140 daga Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kazalika yayin samamen, an gano wani wuri mai kama da masana’antar kera bama-bamai, yayin da kuma wasu daga cikin mambobinsu ciki har da mata da kananan yara su ka mika wuya.

Sojoji sun kuma ce sun sami nasarar tarwatsa gungun mutanen a cikin irin kokarin da su ke yi na kakkabe yankin Arewa ta Tsakiya daga ayyukan ‘yan ta’adda.

Idan za a iya tunawa, a shekara ta 2009 ne aka tarwatsa kimanin mutum 3,500 ’yan wata kungiyar a garin da suka kira da Darus Salam a wani gari mai nisan kilomita 30 daga garin Mokwa na Jihar Neja.

Lamarin ya faru a wancan lokacin ne jim kadan da fara fada tsakanin dakarun Najeriya da ’yan ta’addan Boko Haram a garin Maiduguri na Jihar Borno wanda ya yi sanadiyyar rasa ran kimanin mutum 1,000 a wancan lokacin.

Masana harkar tsaro dai na ci gaba da nuna fargaba kan yadda kungiyar take ta kokarin tara makamai wanda ke alamta yiwuwar su fara kai hare-hare, sabanin yadda aka same su a shekarar 2009.

A wata sanarwa, Babban Jami’in Rundunar Tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce a ci gaba da kai hare-haren da suke yi a yankin, sojojin sun kuma samu nasarar kwace makamai da albarusai da dama.

Enenche ya ce, “Bayan wasu munanan hare-haren da muka kai kan maboyar masu garkuwa da mutane, ’yan kungiyar Darul Salam ciki har da mata da kananan yara sun mika wuya ga rundunarmu da ma na sauran jami’an tsaro da muka jibge a Karamar Hukumar Uttu ta Jihar Nasarawa”.

Ya kara da cewa sun kuma gano abubuwan fashewa da dama a wurin, ciki har da na’urar kera harsasai, na’aurar harba bama-bamai guda shida, buhun takin zamani daya, rabin buhu na hodar bindiga, gurneti kirar gida, na’urar hada bama-bamai guda daya, da dai sauransu.

Tuni dai ya ce suka tarwatsa sansanonin yayin da su ka ci gaba da sinitiri a dazukan da ke da makwabtaka da wurin domin farautar masu yinkurin tserewa.

Rahotanni dai na nuna cewa in banda Jihar Kwara, kusan dukkannin ragowar jihohi biyar na Arewa ta Tsakiya sun yi ta fama da matsalolin tsaro iri-iri a mabanbantan yanayi.

Ko a watanni hudu da suka gabata sai da Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya bayyana damuwarsa kan sake bayyanar kungiyar ta Darus Salam wacce ya alakanta da yawan kashe-kashe da hare-haren da ake kaiwa a jihar.

A wancan lokacin dai, kungiyar ta Darus Salam ta yi ikirarin cewa ba ta dauke da wasu makamai kuma ba kungiyar ta’addanci ba ce, inda suka ce sun shafe sama da shekaru 16 kafin daga bisani a tarwatsa su.