✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun zagaye dajin da aka kai daliban da aka sace

Fadar shugaban Kasa ta ce dalibai 10 ne a wurin ’yan bindiga, bincike ya gano 668 sun bace

Fadar Shugaban Kasa ta ce sojoji sun zagaye dajin da ’yan bindiga suka kai daliban da suka sace daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara (GSSS Kankara) Jihar Katsina.

Kakakin Shugaban Kasa, Garbar Shehu ya cewa an turo zaratan sojoji kasa da na sama domin nemo tare da ’yan sanda na musamman da Babban Sifeton ’yan sanda ya bayar da uarnin aikawa.

“Gwamantin Tarayya ta ce dakarunta sun yi wa dajin da masu garkuwa da mutanen suka ajiya yaran kawanya”, inji shi.

Hadimin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa yara 10 ne ke hannunun ’yan ta’addan.

Ya ce daliban da suka kubuta daga hannun masu garkuwa da mutanen sun ce yara 10 suka rage a hannun maharan.

Tuni dai Shugaba Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya isa garin Kankara inda ya gana da kwamandojin rundunar da binciken aikin ceto daliban.

Iyayen dalibai na tattaunawa bayan ’yan bindiga sun kai harin.

Dalibai 668 ne suka bace —Bincike

Kawo yanzu dalibai 668 ne ba asan inda suke ba bayan harin ’yan bindigar.

Binciken Aminiya ya gano daga rajistar makarantar a ranar Lahadi cewa dalibai 1,047 ne ke makarantar lokacin da ’yan bindigar suka yi mata dirar mikiya da tsakar dare suka fara musayr wuta da jami’yan tsaron da ke gadin ta.

Majiyarmu ta ce “bangaren karamar sakandaren makarantar na da ajujuwa shida JSS 1A, na da dalibai 58, 1B dalibai 62 saia 1C mai dalibai 64; JSS 2A dalibai 74, 2B kuma 79 sannan a 2C akwai dalibai 75.

“Bangaren babbar sakandare kuma ajujuwa bakwai na: SS1A na da dalibai 97; 1B kuma 108; 1C 106 sannan 1D akwai dalibai 118. Akwai kuma dalaibai 74 a SS 2A, 74; SS2B dalibai 79 sai kuma SS2C dalibai 80, jimilla dalibai 1074 ke nan.”

Mazauna garin Kankara a lokacin da dakarun Sojin Sama suka isa garin domin aikin ceto daliban da aka yi garkuwa da suMajiyar ta ci gaba da cewa daliban aji ukun karamar sandare da na aji ukun babbar sakandare sun riga sun kammala jarabawarsu ta fita sun koma gida kafin faruwa lamarin.

Aminiya ta gano cewa dalibai 270 ne aka ceto a makarantar a ranar harin da ’yan bindigar suka kai.

Washegari (Asabar) adadin daliban da suka ya karu zuwa 406 bayan wasu daga cikinsu da suka tsere zuwa cikin daji sun dawo, iyayen wasu kuma suka kira suka sanar da hukumar makarantar cewa ’ya’yansu sun koma gida.

Sai dai sabanin dalibai 668 da binciken Aminiya ya gano sun bace, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce dalibai 333 ne ba a gani ba.

Wasu daga cikin iyayen daliban GSSS Kankara

Iyayen daliban Katsina na roko a ceto ’ya’yansu

Iyayen daliban da suka zanta da Aminiya sun roki gwamnati ta gaggauta yin duk abin da ya kamata domin tabbatar da ganin an ceto ’ya’yan nasu.

“Abin na da tayar da hankali. Yara ne ’yan shekara 12 zuwa 16 aka jefa cikin wannan mawuyacin hali. Mun kasa barci ko cin abinci saboda ba mu san inda suke da kuma halin da da suke ciki ba”, inji Alhaji Isma’l Kafur.

Ya ci gaba da cewa “Shekarun dana 14 kuna yana SS1, akwai kuma wasu yara hudu daga garinmu, Kafur, da ba a gani ba.”

Ya ce ya ga daya daga cikin daliban da ya kubuta daga ’yan bindigar, don haka ya roki gwamnatin jihar da ta matsa kaimi wajen ceto dalibai, amma ya ce a guji yin amfani da karfi wajen yin hakan.

Abubakar Ayuba Gozaki ya ce ’ya’yansa biyu Nasir da Salahuddeen na daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su.

“Da na koma da kayansu gida jiya, sai na ji kamar gawarwakinsu na kai, mahaifiyarsu da ’yan uwa na ta koke-koke, shi ya sa na sake dawowa in gani ko za mu ji wani bayani da zai kwantar da hankali”, inji shi.

Mahaifin daliban da ba gani ba ya yi kira da a yi amfani da diflomasiyya wurin ceto daliban domin “idan aka yi amfani da kari kadai za a kashe ’ya’yan namu. Saboda haka muke rokon gwamnati kar ta yi amfani da karfi.”

Iyayen daliban suna sauraron bayani bayan harin

Zan jagoranci ceto su inda an yarda —Mahaifi

Daya daga cikin mahaifin daliban da aka yi garkuwa da su, Abdurrazak Sani, wanda ya ce shi kwamandan ’yan banga ne a Jaibir, Karamar Hukumar Funtua, ya ce a shirye yake ya jagoranci neman yaran.

“Da tambaya ko an yi wani abu sai aka ce min babu abin da aka yi. Na bukaci wasu daga cikin jami’an tsaron su zo mu bi sawun inda aka bi da yaran amma suka ce ba a ba su izini ba tukuna. Daga nan sai na bukaci ’yan banga su zo mu ce, amma suka ki.

“Daga nan sai na dauki yaron da muka zo tare da shi muka bi hanyar a kan babur, inda muka tsinci wasu abubuwa da suka hada da kayan dalibai, cocila, sabulai da wasu abubuwa da muka dawo da su makarantar”, inji shi.

Ita kuma Hajiya Fa’iza Hamza Kankara, wadda ke cikin tashin hankali, ta ce a matsayinta na uwa, ta kasa cin komai ko rintsawa tun lokacin da ta samu labarin abin da ya faru.

Hajiya Fa’iza ta roki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari su kawo musu dauki su ceto dalaiban da aka yi garkuwa da su.

Wata mahaifiya da Aminiya ta zanta da ita ta ce ta tilasta wa ’ya’yanta biyu su koma makaranta a daren a abin ya faru duk da cewa sun yi ta rokon ta su kwana a gida.

“Sun yi ta roko na cewa za su kwana a gida amma na tilasta su suka koma makaranta ga shi babu wanda ya dawo a cikinsu. Laifina ne abin da ya faru da su”, inji ta.

Alamar shiga garin Kankara

Za mu ceto sun na gaba kadan —Ministan tsaro

Sakamakon harin na GSSS Kankara tawagwar Gwamnatin Tarayya ta ziyarci jihar domin jajantawa da ba da tabbacinn ceto daliban.

Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi ne ya ba da tabbacin inda ya yi bayanin cewa tuni ya jagoranci zaman hukumomin tsaro domin tsara yadda za a ceto yaran cikin sauki ba tare wata asara mai girma ba.

Ya yi bayanin ne a lokacin da ya jagoranci Manyan Hafsoshin Tsaro, Mai Bayar da Shawara kan Tsaron Kasa, Babagana Monguno da Shugaban ’Yan Sanda, Mohammed Adamu zuwa GSSS Kankara domin jajanta wa iyayen daliban da hukumar makarantar da kuma ba su kwarin gwiwa.

Magashi wanda ya ji jaje a madadin Shugaba Buhya ce hukumomin tsaro sun yi nisa wurin tattara bayanai kuma za su yi aiki wurjanjan domin ceto daliban daga hannun masu garkuwar.

An yi zanga-zanga a Katsina

Harin ’yan bindiga a makarantar ya haifar da zanga-zanga da wata mata ta jagoranta domin kira da a gaggauta ceto daliban.

Wani mazaunin Kankara ya ce da farko masu zanga-zangar sun watse da suka ga motocin ’yan sanda na tunkarar su a kusa a tashar motar garin.

Sai dai ya ce daga baya sun sake taruwa inda suka yi maci zuwa makarantar tare da kira da a ceto daliban.

 

Dalibai 333 suka bace —Masari

A jawabinsa, Gwamna Aminu Masari ya ce dalibai 333 ne suka bace daga cikin dalibai 839 da ke makarantar lokacin da aka kai harin.

Ya ce ya umarci hukumar makarantar da ta bude sabuwar rajistar dalibai ta kuma kira dukkanin iyayen daliban makarantar ta waya domin gano hakikanin adadin daliban da suka bace.

Masari ya kuma ba da umarnin rufe daukacin makarantun kwana da ke jihar.

Gwamnan ya kuma yi ganawar sirri da tawagar tsaron Gwamnatin Tarayya da suka ziyarci jihar.

UNICEF ta yi tir da harin

Tuni dai Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi tir da harin tare da kira da a gaggauta sako daliban ba tare da wani sharadi ba.

Babban Daraktar UNICEF a Yammaci da Tsakiyar Afirka Marie-Pierre Poirier ta ce: “UNICEF a damu matuka da wannan aiki na ta’addanci. Kai wa makarantu hari tauye hakkin yara ne.

“Wannan matashiya ce da ke nuna garkuwa da kananan yara da cin zarafinsu na kara yaduwa a Arewacin Najeriya”.

 

Majalisa ta yi tir da harin GSSS Kankara

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Faskari, Kankara, Sabuwa, Murtala Isah Mai Nauyi ya yi Allah-wadai da harin.

Ya ce harin babban ta’addanci ne da kuma tauye hakkin dan Adam ne.