✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji za su iya kawo ƙarshen matsalar tsaro — Kwankwaso

Tsohon gwamnan, ya ce jam'iyyar NNPP ce kaɗai amsar 'yan Najeriya.

Tsohon Ministan Tsaro, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce sojoji za su iya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ƙasar nan ke fuskanta.

Jagoran jami’yyar NNPP na ƙasa, ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin zartarwa na jami’yyar a Abuja.

Ya ce duk da cewa haƙƙin Gwamnatin Tarayya ne, ta magance matsalar tsaro, amma ’yan Najeriya na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar bai wa hukumomin tsaro muhimman bayanai.

“A matsayina na tsohon ministan tsaro kuma tsohon babban jami’in tsaro na Jihar Kano na tsawon shekara takwas, wanda ya yi gwagwarmayar siyasa, na yi imanin tukarar ƙalubalen tsaro na hannun gwamnatin tarayya.

“Muna ganin yadda jihohi ke ƙirƙiro jami’an tsaro. Wani lokaci abun ya ba ka dariya. A halin da ake ciki a Najeriya sojoji ne kaɗai za su iya kawo ƙarshen matsalar tsaro.

“Kuma dole ne kowa ya haɗa kai don ganin an samu zaman lafiya a ƙasar nan.

“Wasu daga cikinmu da ke k5auyuka suna ganin yadda mutanenmu suke zuwa gonaki. Yanzu kuma ba sa iya zuwa gona. Ana korar su daga ƙauyuka da garuruwansu.

“Masu laifi da ’yan bindiga na sace ’ya’yanmu kullum,” in ji shi.

Kwankwaso, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya ce jam’iyyarsa tana da tsarin da za ta bi don magance matsalolin da suka addabi Najeriya.

Ya ce, jam’iyyar NNPP ita ce kawai mafita ga ’yan Najeriya, inda ya ce jam’iyyar APC da PDP sun gaza.

Da yake jawabi, Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano, ya buƙaci ‘yan jam’iyyar da su kasance masu sadaukar da kai da kuma yin biyayya ga jami’yyar.