✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sun yi garkuwa da jariri, suna dukan mai jego don a ba su N50m

’Yan bindiga sun yi garkuwa da jaririya sabon haihuwa tare da tsare mahaifiyarta mai danyen jego suna dukan ta domin a ba su kudin fansa

’Yan bindiga sun yi garkuwa da jaririya sabon haihuwa sannan suka tsare mahaifiyarta mai danyen jego suna lakada mata duka domin a ba su kudin fansa Naira miliyan 50.

Mai tsohon cikin, ta fada hannun ’yan bindiga ne tare ’yan uwanta, a bayan ta je duba mahaifiyarta da ke fama da rashin lafiya a unguwar Mando da ke Kaduna.

Mijinta ya shaida wa wakiliyarta, Mohammed Alabi, cewa, “Ranar 2 ga watan Agusta matata ta haihu a hannun masu garkuwa da mutane ba tare da ita ko jaririn sun samu kulawar likita ba.

“Abin takaicin shi ne mun samu labarin cewa sukan zane matar tasa kuma suna azabtar da su.

“Muna cikin tashin hankali, shi ya sa muke rokon duk wanda Allah Ya hore wa, ya taimaka a sako su.”

Mahaifin mai jegon, Malam Abdulwahab Yusuf, ya ce ’yan bindiga sun kutsa cikin gidansu ne da misalin karfe 1 na dare a ranar da suka yi garkuwa da ’ya’yan nasa.

“’Ya’yana mata na kula da lafiyar mahaifiyarsu, amma abin takaici, ranar babbar yayarsu mai tsohon ciki ce ta zo daga gidan mijinta domin duba ta, ’yan bindiga suka shigo cikin gidanmu suka sace su.

“Da farko sun nemi a ba su Naira miliyan 140, amma yanzu sun rage zuwa miliyan N50.”

“Gaskiya muna cikin tashin hankali, yanzu matata da a baya take iya yin tafiya da kanta, tun bayan faruwar al’amarin ta koma sai a keken guragu.

“Kwanan nan aka yi mata tiyata, ni kaina ina cikin matsala, ni kadai na san yadda yake ji a jikina duk lokacin da dare ya yi,” in ji shi.

Wan wadanda aka yi garkuwa da su, , Kabiru Yusuf, ya ce, “Sun shaida min cewa ana gallaza musu azaba kuma shugaban ’yan bindigar na barazanar tafiya su bar su a wurin.

“Kullum rokon su muke yi, mun sayar da duk abin da muka mallaka, amma bai kai abin da suke nema ba.”

Don haka yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta tarayya da kungiyoyin jinkai da mawadata da su kawo musu dauki domin ceto rayuwar kannen nasa.