✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Surutai ba za su sa mu tattauna da ’yan bindiga ba —El-Rufai

El-Rufai ya ce tattaunawa da biyan kudaden fansa ga ’yan bindiga ba su sa sun daina ba

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi raddi ga sukar da ake masa saboda ya ki tattaunawa da ’yan bindiga da suka yi garkuwa da dalibai a Jiharsa domin ceto daliban.

El-Rufai ya ce duk da cewa a baya ya soki tsohuwar gwamnatin Shugaba Jonathan saboda ta ki tattauna da kungiyar Boko Haram don ta sako daliban Makarantar Chibok, ba zai sa ya canza matsayi ba na ‘babu tattaunawa, babu biyan fansa’ ba.

Ya bayyana hakan ne bayan bullar bidiyon hirar da aka yi da shi a 2014, inda yake caccakar Jonathan saboda kin tattaunawa da kungiyar Boko Haram domin ceto ’yan matan Chibok.

A cewarsa, ko sau nawa za a yada bidiyon da surutan da mutane za su yi a kai, gwamnatinsa na kan bakarta ta rashin tattauanawa ko biyan kudin fansa ga ’yan bindiga.

Martanin nasa na zuwa ne kuma washegarin da aka tsinci karin gawarwarki daliban  Jami’ar Greenfield da aka yi garkuwa da su, da kuma sakin bidiyon ragowar dalibai 29 na Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Jihar.

El-Rufai ya ce bayyana kisan gillar da masu garkuwar suka yi wa daliban Jami’ar Greenfield da cewa “Yunkuri ne na tilasta wa gwamnati jingiye matsayinta na rashin tattaunawa ko biyan ’yan bindiga kudin fansa.”

A hirar da aka yi da shi a 2014, El-Rufai ya ce tun da hakkin gwamnati ne ta kare rayukan jama’a, ya kamata ta yi duk abin da ya kamata, har da tattaunawa da Boko Haram, domin kubutar da daliban Chibok a raye.

Sai dai a takardar da kakakinsa, Muyiwa Adekeye ya fitar, El-Rufai ya ce, “Yanzu al’amura sun canza kuma a bayyane yake cewa mafita ita ce hukumomin gwamnati ta yi amfani da karfinta ta dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda.”

A cewarsa, babu yadda za a yi gwamnatin jiharsa da ke neman gani bayan matsalar ta rika dibar kudade tana ba wa ’yan bindiga suna kara karfi, alhali Gwamantin Tarayya tana kokarin muttsuke su.

Ya ce, “Watakila shekarun da aka dauka daga 2014 zuwa yanzu suna sa an manta cewa a farkon wancan lokaci gwamnatin ta yi ta jan kafa, tare da kin yarda cewa an sace daliban, shi ya sa aka yi mata ca.

“Daga 2014 zuwa yanzu, tattaunawa da biyan kudin fansa ba za su yi tasiri ba, duk makudan kudaden da ake kashewa wurin biyan kudin fansa ba su yi amfani ba.”

“Abin da ya kamta shi ne kawai gwamnati ta yi amfani da karfinta wajen dakile ayyuka ta’addanci.”

Ya ci gaba da cewa, “Tun a shekarar 2015 matsalar satar shanu, garkuwa da mutane da tarwatsa al’ummomi suka addabi musamman yankin Arewa maso Yamma.

“Hakan ta sa gwamnatocin wasu jihohi tattaunawa da yin afuwa ko biyan kudin fansa ga ’yan bindiga da nufin kawo karshen matsalar amma hakar ba ta cimma ruwa ba.

“Maimakon kawo karshen matsalar, sai ’yan bindigar suke kara matsa lamba don a rika dibar kudin jama’a ana ba su, wanda kuma hakan ba zai amfani al’umma ba.”

Don haka a cewarsa, “Sabanin sabanin 2014, lokacin da satar mutane ba ta zama ruwan dare ba, yanzu abin ya canza — an tattauna da su, an biya kudaden fansa amma sun ki su daina.

“Saboda haka yana da kyau duk lokacin da abubuwa suka canza, dole mutum ya sauya matsayarsa a kansu,” amma ba a rika biyan ’yan bindiga kudade ana karfafa su ba.”

El-Rufai ya ce, “Shawarar da wani ya bayar a 2014 ba zai taba zama mafita ga matsalar da riga ta dade da rikida ba, ko da sau na za a yada bidiyon da ake magana a kai.”