✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Suu Kyi ta gurfana a kotu kan cin amanar kasa

Karon farko da Shugabar Myanmar da aka hambarar ta fito bainar jama'a bayan juyin mulki.

Hambararriyar Shugabar Kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi ta bayyana a gaban kotu a ranar Litinin, domin fuskantar tuhumar tunzura jama’a da cin amanar kasa.

Karon farko ke nan da aka ga Suu Kyi mai shekara 75 a bainar jama’a tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi mata a farkon watan Fabrairu.

Zargin cin amanar kasa da ake mata a yanzu shi ne tuhuma mafi girma da ta fuskanta. Ana kuma zargin ta da karya dokar tsare sirrin kasa.

Lauyanta, Thae Maung Maung, ya ce lauyoyi sun sami damar ganawa da ita gabanin fara zaman kotun inda suka tattauna batun shari’ar.

Ya fada wa Kamfanin Dillancin Labaran Jamus, DPA, cewa Suu Kyi tana cikin koshin lafiya kuma za ta sake bayyana gaban shari’a a ranar 7 ga watan Yuni.

Lauyan ya ce an tanadar da zauren kotun musamman domin sauraron karar a babban birnin Naypyidaw, da ke kusa da gidan Suu Kyi.

Zanga-zangar kyamar juyin mulkin soji a Myanmar ya gamu da mummunan martani daga sojojin da suka hamabarar da gwamnatin Suu Kyi inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu.

Wata kungiya mai sa ido kan fursunonin siyasa ta ce zuwa yanzu an kashe akalla mutum 818, wasu fiye da 5,300 kuma ana tsare da su.