✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta antaya wa mijinta ruwan zafi saboda ya ki zuwa biki da ita

Tuni jami'an 'yan sanda suka cafke matar suka tsare ta.

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta cafke wata mata mai bisa zargin sheka wa mijinta ruwan zafi saboda bai je biki da ita ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Litinin.

Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Disamba, inda aka kama wadda ake zargin bayan da rundunar ta samu labarin faruwar lamarin.

Ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma mijin matar na kwance a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Tun da farko wata majiya ta shaida wa NAN cewa matar ta fusata da mijin, wanda ya halarci daurin auren abokinsa amma ya ki tafiya da ita.

NAN ta ruwaito cewa rikici ya barke a tsakanin ma’auratan, lamarin da ya kai ga matar debo tafasasshen ruwan zafi ta kwara wa mijin nata.

Tun da fari ma’auratan sun shirya zuwa wurin bikin tare, amma daga baya mijin ya sauya shawarar tafiya shi kadai.