✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta maka saurayinta a kotu kan yada tsiraicinta a Facebook

Saurayin ya yi ea budurwar ta shi barazana idan ba ta saya masa waya ba.

Wata budurwa a Kano ta maka saurayinta a kotun Shari’ar Musulunci kan barazanar yada hoton tsiraicinta a Facebook.

’Yan sanda sun gurfanar da matashin a gaban kotun mai shari’a Nura Yusuf Ahmad, da ke unguwar Gama PRP a Karamar Hukumar Nassarawa, bisa tuhumar tsoratarwa.

Mai gabatar da karar, Aliyul ‘Abidin, ya shaida wa kotun cewa budurwar ta janye sakamakon wanda ta shigar da karar a kansa saurayinta ne.

An zargi matashin da yunkurin bata wa budurwa suna, bayan ya yi mata barazanar yada hoton tsiraicinta a Facebook, wanda hakan na iya bata mata suna.

Tun da farko saurayin ya yi wa budurwar barazana ne domin ta saya masa waya.

Sai dai bayan janye kararta, kotun ta sallami matashin da ake tuhuma, inda ta gargade shi kan yi wa mutum barazana.

Barazana yada hoton tsiraicin ’yan mata a kafafen sada zumunta lamari ne da ke yaduwa kamar wutar daji.

Sai dai malamai ma ci gaba da jan hankalin matasa kan illar yada hotunan batsa a kafofin intanet.