✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta’ammali da kwayoyi: An haramta wa ’yan takara 6 shiga zaben Kano

A daidai lokacin da zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano na ranar 16 ga watan Janairu ke kara matsowa, Hukumar Zabe ta Jihar (KANSIEC) ta haramtawa…

A daidai lokacin da zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano na ranar 16 ga watan Janairu ke kara matsowa, Hukumar Zabe ta Jihar (KANSIEC) ta haramtawa ’yan takara shida shiga zaben.

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bayan da sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna suna ta’ammali da miyagun kwayoyi.

KANSIEC dai ta ce ta kirkiro gwajin ne na dole a kan dukkan ’yan takarar Ciyamomi da Kansiloli la’akari da yadda matsalar ta’ammali da kwayoyin a Jihar ke dada kamari.

Shugaban Hukumar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da Aminiya kan shirye-shiryen da hukumar take yi na zaben.

Ya ce, “Bayan gudanar da gwajin kwayoyin da Humumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta jagoranta, akan dukkannin ’yan takarar kujerun Ciyamomi 44 da na Kansiloli 484, shida daga cikinsu binciken ya tabbatar da suna ta’ammali da kwayoyin kuma mun haramta musu shiga zaben.

“Duk wadanda aka samu da alaka da kwayoyin masu takarar Kansiloli ne, babu ko daya daga cikinsu da yake neman kujerar Ciyaman.

“Jam’iyyun da abin ya shafa sun yi sa’a cewa har yanzu suna da wannan makon da muke ciki domin su maye gurbinsu da wasu ’yan takarar, saboda ba za mu bar ’yan kwayar su tsaya ba,” inji Sheka.

Shugaban na KANSIEC ya kuma ce Hukumar ta kirkiro gwajin ne domin tabbatar da cewa an rage yawan masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

Farfesa Sheka ya kuma ce suna da kwarin gwiwar cewa matakin zai taka muhimmiyar rawa wajen zama izina ga matasa masu burin tsayawa takarar siyaya a nan gaba saboda tsoron haramta musu takara.

To sai dai rahotanni sun ambato wata majiya a NDLEA na cewa adadin mutanen da binciken ya nuna suna ta’ammali da kwayoyin ya kai 20 ba shida ba kamar yadda KANSIEC ta yi ikirari, ciki kuma har da ’yan takarar jam’iyyar APC mai mulki.