✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta’aziyya: Buhari ya ziyarci iyalan Yar’adua a Kaduna

Buhari, wanda ya bayyana rasuwar ta a matsayin rashi mai radadi, ya roki Allah da ya karbi ayyukan ta na alheri.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan Marigayi Yar’adua game da rasuwar Hajiya Rabi, suruka ga tsohon amininsa kuma abokin karatunsa, Marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua.

Shugaba Buhari, wanda ya je Kaduna a ranar Asabar don bikin yaye dakarun soji a Kwalejin Horas da Dakarun Soji ta Najeriya (NDA), ya kuma dauki wani lokaci daga jadawalin aiki don ziyartar gidan Yar’adua inda Hajiya Binta’ Yar’aduwa, matar marigayi Janar din kuma ‘yar marigayiya Hajiya Rabi ta tarbe shi.

Shugaban kasar ya ce marigayiya Hajiya Rabi ta yi rayuwa mai albarka wacce ta cancanci a yi koyi da ita, don a cewarsa ta bar tarihi wanda ba za a manta da shi ba a rayuwar dimbin wadanda suka kusance ta.

Buhari, wanda ya bayyana rasuwar ta a matsayin rashi mai radadi, ya roki Allah da ya karbi ayyukanta na alheri.

A ranar Asabar aka yi zaman makoki na kwanaki uku da rasuwar Hajiya Rabi.