✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aboki ya kashe abokinsa bayan cacar baki

Ana zargin wani matashi mai suna Aliyu Aminu wanda aka fi sani da Haidara, mai kimanin shekara 17 sha bakwai da kashe abokinsa mai suna…

Ana zargin wani matashi mai suna Aliyu Aminu wanda aka fi sani da Haidara, mai kimanin shekara 17 sha bakwai da kashe abokinsa mai suna Aliyu Shehu mai shekara 17 da suke zaune  a unguwa daya a sanadadiyyar cacar baki a tsakaninsu da kuma zugar abokai.

Lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe tara na safe, a Unguwar Gangaren Kwadi da ke Tudun Wadan Zariya a Jihar Kaduna.

Wakilinmu wanda ya ziyarci unguwar ya yi kokarin jin ta bakin iyayen marigayin amma sun ce ba za su ce komai ba saboda ba su a wurin da abin ya faru. Haka iyayen wanda ake zargin da kisan, sun ki cewa komai, illa suna nuna rashin jin dadinsu da nuna juyayi a kan abin da ya faru.

Aminiya ta samu labarin wadansu sun yi kokarin raba samarin, amma saboda abokai suna zuga su kuma ajali na kira sai da suka fafata a tsakaninsu inda daya ya kashe daya.

Wata majiya ta ce marigayi Aliyu Shehu ya ce wa wanda ya kashe shi Aliyu Haidara zai tura abokansa domin su yi maganinsa idan ya ci gaba da yi masa gani-gani. Shi kuma Haidara sai abokai suka ce masa idan ba ka tsaya ka nuna masa cewa bai isa ba, to wannan fadan ba zai kare ba, duk inda ya gan ka sai ya nuna maka raini, don haka ka tsaya ka yi maganinsa. 

Majiyar ta ce hakan ne ya sa suka zaga bayan gari suka je wani fili da ake kira filin Sale Maidoki da wadansu ke kira da filin Alaliya domin su goge raini, a nan ne suka harde da kokowa, inda Aliyu Haidara ya dauki marigayi Aliyu Shehu ya doka kansa a kasa, wanda haka ya yi sanadiyar karyewar wuyansa, daga nan ne aka dauke shi zuwa gida, aka wanke masa raunin da ya samu a keyarsa, ana shirin kai shi asibiti sai aka ji ya yi wani irin numfashi, daga nan sai rai ya yi halinsa. 

Majiyar ta ce an sanar da ’yan sanda abin da ya faru, suka zo da mota suka dauki gawar suka kai asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa, sannan aka dawo aka ba iyayen gawar domin yi masa jana’iza. Kuma wadanda suka yi masa wanka sun ce wuyansa ne ya karye wanda hakan ya yi ajalinsa.

Wata majiya a unguwar ta shaida wa wakilinmu cewa iyayen wanda ya yi kisan sun yi kokarin ziyartar gidan su marigayi domin yi ta’aziyya da jajanta musu, amma sai iyayen marigayin suka ki yarda su matso kusa da inda suke, suka hau su da hargowar cewa ba za su taba yarda su kyale wannan abu da ya faru ba.

Babban Jami’in ’Yan sandan Tudun Wada, Zariya, ASP Abdullahi Yusuf ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yaron da ake zargi da kisan ya gudu, amma sun gayyaci mahaifinsa da shaidu, domin tattara bayanai, kuma sun baza komarsu domin farauto wanda ake zargi da kisan.