✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aiki Buhari yake so ba sata ba – Sani Zangon Daura

Tsohon Ministan Aikin Gona, Alhaji Sani Zangon Daura ya ce ya dace ’yan Najeriya su amince Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin takarar shugabancin Najeriya…

Tsohon Ministan Aikin Gona, Alhaji Sani Zangon Daura ya ce ya dace ’yan Najeriya su amince Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2019 domin ya ceto kasar nan daga wahala zuwa walwala domin jin dadin kowa ba kamar yadda ya gada daga gwamnatin da ta wuce ba.

Alhaji Sani Zangon Daura, ya shaida wa Aminiya cewa, “Na yi matukar farin ciki da Shugaba Buhari ya ce zai sake yin takara don neman a zabe shi a 2019. Domin an dade ban ga mutum mai farin jini da rikon amana da son yi wa jama’a aiki kamarsa ba. Domin duk abin da ya sa a gaba, yana matukar jajircewa, mutum ne mara wargi ko kadan. Haka ta sa wata mujalla mai suna DRUM ta yi masa lakabi da “Mai saukin kan da ba a gane ba,” lokacin da ya zama Shugaban kasa na mulkin soja. A cikin duk wadanda suke son yin takara da Buhari a jam’iyyu daban-daban, wane ne zai iya yin takara da shi? Shi yana son kasa fiye da kansa, yana da rikon amana da uwa-uba kuama da bin doka da oda.”

 Alhaji Sani wanda shi ne danmasanin Daura ya bukaci, ’yan Najeriya su rungumi Buhari, su goya masa baya don ya ci zabe a karo na biyu, saboda ba ya da tabo, kuma a cikin shekara uku an samu ingantuwan zaman lafiya ganin a da duk wanda zai je masallaci ko coci ko kasuwa ko janna’iza a cikin tsoro yake. 

danmasanin Dauran ya ce, “Shugaba Buhari ya hau mulki ne don ya yi aiki, ba don ya yi sata ba, a koma bin doka da oda, don haka idan mutane na son gaskiya, su fito su jefa masa kuri’a ya kawo sauyi tare da ceto Najeriya daga masu halin bera.”