✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alarammomi sun zargi gwamnatin Kwankwaso da rashin cika musu alkawari

Shugaban wata kungiyar alarammomi a Jihar Kano mai suna Hizburrahman Fi Tilawatil kur’ an, Alaramma Tukur Ladan, ya zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Rabi’u…

 Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar KanoShugaban wata kungiyar alarammomi a Jihar Kano mai suna Hizburrahman Fi Tilawatil kur’ an, Alaramma Tukur Ladan, ya zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da rashin cika musu alkawarin da ta yi na taimaka musu a farkon hawanta karagar mulki.
Alaramma Tukur ya bayyyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce “Ina mamakin gwamnatin da ake yayatawa cewa mai taimakon jama’ a ce, amma ga shi ta kasa taimaka mana da komai, har ta shiga shekararta ta uku a kan mulki.”
Ya ce duk da cewa kwamitin da Gwamnan ya kafa ya je ya duba wurin karatun alarammomin da inda suke koyo da koyar da sana’ar gyaran manyan motoci, tare da alkawarin za a tallafa musu, har yanzu ba a taimaka musu da komai ba.
Ya ce “Sai dai mu ji ana cewa yau an taimaka wa wanzamai ko mahauta ko wasu masu wata sana’a, amma alarammomi wadanda muka bayar da gudummawar addu’a da kuri’a ga kafuwar gwamnatin an kyale mu, mun zama ’yan kallo kawai.”
Shugaban alarammomin ya zargi manyan daraktocin gwamnatin jihar da danne takardunsu na neman taimako. “Ina kyautata tsammanin Gwamna bai san abin da yake faruwa ba kan manyan ma’ aikatan da suke kawo mana cikas wajen cika mana alkawari.”
Sai ya yi kira ga Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya binciki yadda wasu mukarraban gwamnatinsa ke tafiyar da ayyukan da aka damka musu amana, amma suke kin yi.