✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah (SWT) Ya sa shekarar 2018 ta fi ta 2017 alheri

“Ta zama shekara mafi tsauri ga Nijeriya, ina fata shekara mai zuwa ta zama mafi yalwa.” In ji shuagabn kasa Muhammadu Buhari. “Wani abin kunya…

“Ta zama shekara mafi tsauri ga Nijeriya, ina fata shekara mai zuwa ta zama mafi yalwa.” In ji shuagabn kasa Muhammadu Buhari.

“Wani abin kunya ne a ce a lokacin Kirsimeti ana fuskantar wannan matsala ta kawo kunci. Wannan abin nadama ne, kuma nasan cewa bisa ga hakuri da karfin hali na mutanen Legas da ma mutanen kasa za mu ga wucewar wannan al’amari kuma za mu yi bukukuwan Kirsimeti cikin jin dadi kuma mu shiga cikin sabuwar shekara da fatan samun sauki.” In ji mataimakin shugaban kasa Furofesa Yemi Osinbajo.

Shugabannin biyu sun yi wadancan maganganu ne a lokuta daban-daban tamfar sun hada baki bisa ga irin mawuyacin halin da ’yan kasa suke ciki daf da karshen shekarar da ta gabata. Yayin da Shugaba Buhari ya yi wadancan kalamai na sama lokacin da ya ke karbar ayarin wasu mazauna babban birnin tarayyar Abuja karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya da suka kai masa ziyarar barka da zagayowar Kirsimeti. Shi kuwa mataimakinsa ya yi nasa jawaban ne a jajibirin Kirsimeti, lokacin da ya yada zango a gidan mai na Oando da ke unguwar Lekki da ke Legas, inda ya ga bakar wahalar da masu ababen hawa suke fama da ita wajen sayen man fetur, wahalar da har zuwa farkon sabuwar shekarar nan ake cikinta.

Ba ko shakka shekarar 2017, da muka yi bankwana da ita a ranar Lahadi da ta gabata ta zama shekara mai matukar kunci ta fannoni daban-daban, kama daga kan batun rashin tsaro zuwa matsalar faduwar tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa da fadace-fadacen Fulani makiyaya da manoma da rigingimu masu kama da kabilanci da addini da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da uwa uba rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram da kasar nan take fama da shi tun a shekarar 2009, baya ga matsalolin tafiyar da mulki irin na siyasa da kowa ke da ’yancin fadin albarkacin bakinsa da sunan tsarin mulki ya ba shi dama. 

Kafin in yi nisa a cikin wannan makala ya kamata a takaice in yi waiwaye akan batutwa uku da Gwamnatin Jam’iyyar APC, ta yi wa ’yan kasa alkawarin aiwatarwa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015, su ne !) Yaki da cin hanci da rashawa (2) Farfado da matakan tsaro da na (3) Farfado da tattalin arzikin kasa, kamar dai yadda na ambata su tun farko anan sama. Ba ko shakka akan batun yaki da cin hanci da rashawa a cikin shekarar da ta gabata gwamnatin tarayyar ta ci gaba da himmatuwa wajen zakulo wadanda suka sace kudaden kasar nan, yakin da ya wuce akan ’yan siyasa ko ma’aikatan gwamnati ya kai kan wasu manya da kananan Alkalan kasar nan da wasu Lauyoyi da ake gani tamfar shafaffu da mai ne. Ba ko shakka wannan yaki babban yaki ne bisa ga irin yadda cin hanci da rashawa yake da babbar illar da take kassara duk wani fanni na tafiyar da kasar nan baki dayansa. A kullum dai sabon labari kake ji akan wannan yaki da ba mai karewa ba ne cikin wani dan karamin lokaci, bisa ga la`akari da irin yadda aka yi barnar da ma wadda ake kai yanzu. Cin hanci da rashawar da aka yi a wannan gwamnatin ne ya ci tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Babachir Dabid Lawal da wasu jami`an gwamnatin.

Akan batun yaki don farfado da matakan tsaro, babban yakin da gwamnatin ta sa a gaba tun bayan da ta zo kan karagar mulki yau kusan shekaru 3, shi ne na yaki da ’yan kungiyar Boko Haram da suka bulla a Jihohin Shiyyar Arewa maso Gabas tun a shekarar 2009, kamar yadda na ambata tun farko. Fitnar da a ’yan shekarun baya ta watsu cikin kasa, kai har ma da kasashen makwabtanmu irin su Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi. Amma yanzu musamman a cikin shekarar da muka yi ban kwana da ita yaki da ’yan kungiyar ta Boko Haram kusan ka iya cewa  ya takaita ne a jihohin Borno (inda dama daga can aka faro shi) da Yobe da Adamawa. Daga kuma yadda gwamnatin tarayyar ta dukufa a kai, ka iya cewa a wannan shekarar da yardar Allah za a iya kawo karshensa.

Sauran miyagun ayyukan ta’addancin da gwamnatin tarayyar da sauran mahukunta suka dukufa akai don kawo karshen sun hada da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da sace-sacen shanu da fadace-fadacen Fulani makiyaya da manoma, rikice-rikicen da suka sa Gwamnatin Jihar Binuwai ta kafa Dokar takaita kiwo a dukkan fadin jihar. Akwai kuma annobar fadace-fadace masu kama da addini da kabilanci da kasar nan ta dade tana fama da su, baya ga annobar basa bututn man fetur da ta kwanta a cikin shekarar da ta gabatan kuma ake fatan kwantawarta a wannan sabuwar shekarar da take shekarar yakin neman zaben shekarar badi in Allah Ya kai mu.

Wani babban batu da gwamnatin tarayyar ta sa gaba shi ne na farfado da tattalin arzikin kasa da ya fadi kasa warwas tun a shekarar 2015, kafin shigowarta mulki. Alhamdulillah! Ta wannan fanni ka iya cewa gwamnatin tarayyar ta fara gano bakin zaren, kasancewar a karshen watan shidda na shekarar 2017, Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta bayar da bayanin cewa kasar nan ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga, har tattalin arzikin ya habaka da kashi 0.76 cikin 100. Kazalilka a karshen watan tara ne dai shekarar da ta gabatan, Hukumar ta NBS ta sake bayar da kididdigar cewa tattalin arzikin ya sake habaka da kashi 1.40 cikin 100. Habakar da masana tattalin arzikin kasa suka tabbatar da ita. 

Koda ga al’ummar kasa za su iya tabbatar da cewa a kulli yaumin kayayyakin masarufi da na sauran bukatu farashinsu yana kara sauka. Albarkacin yadda damina ta yi harshe kusan dukkan amfanin gonar da aka noma ya samu gwargwadon iko, ya sanya farashin kayayyakin amfanin gona sun fadi. Sabon tsarin shirin samar da takin zamani na gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kowane buhu daya a kan N5,500, a ko’ina cikin fadin kasar nan, shi ma ya yi tasiri duk da yake wasu manoma sun koka a kan ba su samu takin akan wancan kaiyadadjen farashi ba. 

Masu masana’antu sun cigaba da kokawa a kan karancin wutar lantarki da samun basussuka masu saukin kudin ruwa. A shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta bayar da aikin ginin tashar wutar lantarki ta Mambilah a cikin Jihar Taraba aikin da aka yi watsi da shi sama da shekaru 40, da suka gabata, da fatan ganin an kammala nan da shekaru shidda masu zuwa in Allah Ya kaimu.

Mai karatu, saboda kuracewar fili a yau nan zan tsaya da kai, amma akwai bukatar ka fahimci cewa dukkan mawuyacin halin da kasar nan take ciki musamman wadancan abubuwa guda uku ba abin da za a iya fita daga cikinsu a rana daya ba ne. Don haka aiki ne babba da yake bukatar gudunmuwar kowa da kowa, ta fannoni daban-daban. Da haka nike cewa Allah SWT Ya sa shekarar 2018 ta fi ta 2017 alheri ta kowane fanni. Sai mun sadu a mako na gaba a kan wani batun na shekarar 2018 insha Allah.