✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayarin motocin Jakadiyar Amurka ya kashe yaro a Kamaru

Motocin da ke yi wa Jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin Duniya, Samantha Power, rakiya a ziyarar da take yi a kasar Kamaru, sun kashe wani…

Motocin da ke yi wa Jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin Duniya, Samantha Power, rakiya a ziyarar da take yi a kasar Kamaru, sun kashe wani yaro “bisa kuskure”.
Misis Power ta je Kamaru ne domin goyon bayan kasar a yakin da take yi da kungiyar Boko Haram.
Sai dai daya daga cikin motocin, wadanda ke matukar gudu, ta buge yaron mai shekara bakwai a birnin Mokolo a lokacin yana kokarin tsallaka titi, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
Jakadiyar ta bayyana matukar rashin jin dadinta ga faruwar wannan lamari. Ta ce “na kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan yaron, inda na bayyana alhini ga munmunar al’amarin da ya faru.”
“Duk da cewa nan take likitoci daga wata motar asibiti da take mana rakiya suka fara bai wa yaron magani, amma daga bisani sai rai ya yi halinsa,” inji ta.
Bayan faruwar lamarin ne, jakadiyar ta gana da wasu yara wadanda suke tsire wa rikicin Boko Haram a wani sansanin ’yan gudun hijira.