✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bacewar Dala miliyan 44 daga taskar Hukumar NIA

’Yan Najeriya sun hadu da wani labara mai tayar da hankali a makon jiya, lokacin da aka bayar da rahoton bacewar wata Dala miliyan 44…

’Yan Najeriya sun hadu da wani labara mai tayar da hankali a makon jiya, lokacin da aka bayar da rahoton bacewar wata Dala miliyan 44 daga taskar Hukumar Leben Asiri ta basa (NIA).

Jaridar Daily Trust on Sunday ta bayar da rahoton inda ta ruwaito wasu manyan majiyoyin tsaro suna cewa kudin wanda aka ajiye a taskar Hukumar NIA da ke Abuja an dauke su zuwa wani wuri da ba a sani ba bayan kwana biyu da nada Ahmed Rufa’i Abubakar a matsayin sabon Darakta Janar na hukumar.  

A cewar labarin Gwamnatin Jonathan ta bayar da Dala miliyan 260 ga Hukumar NIA a matsayin kudin tallafi na gaba daya. Kuma a lokacin da Gwamnatin Tarayya ta baddamar da bincike kan kudaden a bara, kudin da kawai aka gano shi ne na Legas, kuma Dala miliyan 44 da ke kwance a ma’ajiyar ta Abuja yana daga cikin sauran kudin na ainihi Dala miliyan 260. An ce wadansu masu barfin fada-a-ji sun matsa wa mubaddashin Darakta Janar na Hukumar Ambasada Mohammed Dauda ya yi amfani da kudin tunda dukiyar Hukumar NIA ce amma ya bi. Kwana biyu bayan Shugaban basa Muhammadu Buhari yam aye gurbin Dauda da cikakken Darakra Janar, sai wata babar motar daukar kudi ta isa ginin na  Hukumar NIA da misalin barfe 6:00 na safe a ranar Juma’a ta dauke kudin zuwa inda ba a sani ba.

 dauke kudin na baya-bayan nan ya hadu da fushin ’yan Najeriya saboda ya zo ne a daidai lokacin da ’yan basa ba su gama farfadowa daga kaduwar da suka hadu da ita ba, kan bwato Dala miliyan 43.4 a wani gida da ke Ikoyi, Legas da Hukumar Yabi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta yi. Hukumar NIA ta ce, kudin nata ne kuma an tanade su ne domin gudanar da wasu ayyukan sirri. 

Wani kwamitin Shugaban basa na mutum uku da Mataimakin Shugaban basa Yemi Osinbajo ya jagoranta ya binciki lamarin a watan Oktoban bara, kuma aka salami Ayo Oke daga mubaminsa na Darakta Janar, wata shida bayan an dakatar da shi.

Jim kadan bayan fitowar wannan labari na baya, manyan jami’an gwamnati sun bayar da bayanai wadanda suka gaza bayar da hujja ko alfanun kwashe kudin daga ma’ajiyar NIA. Kuma sakamakon gazawar hukumar ta musanta ko ta bayar da hujja mai barfi kan hakan, sai Majalisar Wakilai ta yanke wata shawarwarin bincikar lamarin sakamakon bubatar da dan majalisar Diri Duoye ya gabatar yana neman a binciki lamarin.

Majalisar ta ce, batun “Ya nuna mugun halin da harkokin tsaron basar nan ke ciki tare da zubar da mutuncin hukumar a idon jama’a da kuma basashen duniya.”

Muna yaba wa ’yan majalisar kan daukar wannan mataki kuma muna shawartarsu sun gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da duk wanda yak eta doka an hukunta shi domin zama darasi ga saura. Kuma a bayyana wa jama’a sakamakon binciken kwamitin da aka dora masa alhakin gudanar da binciken. Tuni a kwai rahotannin da suke cewa, Hukumar EFCC ta fara yin tambayoyi ga wadansu jami’ai da suke da alaba da kudin. A tabbatar an yi duk bobarin da ya wajaba domin bankado tushen lamarin. Hukumar NIA, babbar hukumar ce da ake girmamawa, amma rahotanni na baya-bayan nan suna nuna yadda mutuncinta yake matubar zubewa. Baya ga haka suna jawo abin kunya tare da nuna yadda hukumar tsaron ta lalace, alhali tana cikin mafiya daukaka.

 Muna sane da cewa Hukumar NIA, galibi tana gudanar da wasu ayyuka na sirri ne, kuma akasarin ayyukanta ba a bayyana su saboda muhimmancins. Amma akwai dokar da ta kafa hukumar, kuma yana da kyau ta riba bin doka a kowane lokaci.

Labarai marasa dadi kamar wadanda ake jinginawa ga hukumar a ’yan watannin da suka gabata suna sa ’yan Najeriya suna yanke bauna daga hukumar.  Bai kamata jami’an gwamnati su mayar da Hukumar NIA saniyar tatsa ba, domin duk kudin da aka ba hukumar domin gudanar da wani muhimmin aiki don haka wajibi ne a gudanar da wannan aiki.

Muguwar dabi’ar nan ta karkatar da kudaden da sauran hukumomin gwamnati ke yi bai kamata a samu haka a irin wannan hukuma mai muhimmanci ba. Hukumar NIA kada ta yarda a riba samunta da irin wadannan labarai da za su zubara mata da martaba. Hukuma ce ta tsaro don haka wajibi ne ta zama abar misali wajen gudanar da ayyukanta. Don haka muna kira ga ma’aikatan hukumar su sauya salon tafiyarsu tare da tabbatar ana gudanar da ayyuka a cikinta kamar yadda doka ta tanada.