✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakala: A dakin Shekarau muka raba Naira miliyan 950 – Aminu Wali

 Kai ka roke ni a yi haka – Shekarau Tsohon Ministan Harkokin Waje Alhaji Aminu Wali, ya ce a uwar dakin tsohon Gwamnan Jihar Kano…

 Kai ka roke ni a yi haka – Shekarau

g Gidan Malam Ibrahim Shekarau da aka yi rabon kuxin a ciki                               Hoto: Daga Sani MaikatangaTsohon Ministan Harkokin Waje Alhaji Aminu Wali, ya ce a uwar dakin tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi a zamanin Shugaba Goodluck Jonathan, Malam Ibrahim Shekarau suka raba Naira miliyan 950 da ya karbo daga Abuja. Ana zargin Wali ya karbo kudin ne daga tsohuwar Ministar Mai Diezane Alison Madueke domin gudanar kamfe din Shugaban kasa zaben bara.
Alhaji Aminu Wali, ya bayyana haka ne a wani gidan rediyo a Kano kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito a ranar Litinin da ta gabata.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) ta gayyaci Aminu Wali a ranar Alhamis din makon jiya, don amsa tambayoyi kan wannan kudi, kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar China ya yi ikirarin karbar kudin kamfe din a matsayinsa na shugaban kwamitin mutum bakwai na Jihar Kano.
Kwamitin yana da wakilan da suka hada da Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Bashir Lado da Sanata Bello Hayatu da Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Alhaji Rabi’u dansharu da Ko’odinetan Kamfe din Goodluck Jonathan, Alhaji Mansur Ahmad. Sai dai ya nanata cewa an dauki kudin ne zuwa uwar dakin Shekarau inda aka raba.
Wali ya ce bai amfana da kudin ba, shi dai ya karbo ne kawai daga Abuja a matsayinsa na mafi girma a cikin kwamitin. Kuma ya ce yana zuwa ya mika kudin ga kwamitin wanda ya raba kudin a gidan Shekarau da ke Kano. Daga cikin wadanda suka gajiyar kudin a cewar Wali, akwai Shekarau da Ahmad da dansharu da Lado da kuma Hayatu.
Tsohon Ministan ya ce Hukumar EFCC ta gayyace shi ne don ya yi bayani kan abin da ya sani kuma an kyale shi ya yi tafiyarsa. Wata majiyar EFCC ta ce hukumar ta gayyaci Shekarau ya bayyana a gabanta don ya yi bayani kan rawar da ya taka wajen rabon Naira miliyan 950 din a ranar Talatar da ta gabata.
Sai dai a martanin da Malam Ibrahim Shekarau ya mayar ya ce Alhaji Aminu Wali ne ya roke shi su raba Naira miliyan 950 a gidan nasa.
Shekarau, wanda ke fadin haka ta bakin kakakinsa, Malam Ghali Sadik, ya ce bai ga kudin da ake magana ba, lokacin da aka kawo su gidansa. “Wali ya tunkare ni a ranar da ya karbo kudin inda ya ce saboda tsaro yana son ya raba kudin a gidana, sai na amince. Ya kawo kudin gidana da misalin karfe 2:00 na dare. Ina cikin dakina da ke sama lokacin da suka shigo, kuma na ci gaba da zama a can har suka kamala rabon. Wali da wasu ’ya’yan jam’iyya suka raba kudin bisa umarnin da aka ba su. Don haka ko kudin ban gani ba da idona,” inji shi.
Tsohon Gwamnan ya tabbatar da samun gayyata daga Hukumar EFCC, inda a matsayinsa na shaida zai je hukumar ya bayyana duk abin da ya sani game da kudin.
Da aka tambayi Ghali Sadik ko tsohon Ministan Ilimin ya amshi nasa kason daga cikin Naira miliyan 950 din, sai ya ce “Malam Shekarau bai gaya min komai a kan haka ba, abin da kawai ya ce, zai amsa gayyatar EFCC din.”
Ya ce, Malam Shelarau yana Legas don wata hidima, amma ya bayar da tabbacin zai je Hukumar EFCC din.
Wata majiya a ofishin Hukumar EFCC da ke Kano ta shaida wa Aminiya cewa Aminu Wali ya kai Naira miliyan 45 ga hukumar.
A Alhamis din makon jiyan EFCC ta kuma yi tambayoyi ga Dokta Nurudeeen Mohammed wanda aka yi zargin ya karbi Naira miliyan 500 daga kudin kamfe din, kuma bayanai sun ce kudin na daga cikin wadanda tsohuwar Ministar Mai Misis Diezani Alison-Madueke ta kasafta domin babban zaben bara.
Jami’an na FECC sun kuma tuhumi shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Ribas Mista Ntufam John Okon bisa zarginsa da karbar Naira miliyan 500 daga cikin kudin kamfe din da suka kai Dala miliyan 115. An kama Okon ne a Kalaba a ranar Alhamis.
Shi ma tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani-Kayode ya gurfana a gaban Hukumar EFCC a ranar Litinin bisa zargin ya karbi Naira miliyan 840 don kamfe din zaben bara. Kayode ya bayyana a hedkwatar EFCC ne bayan jami’an hukumar sun kai masa hari a ranar Juma’ar da ta gabata a gidansa.
Sauran wadanda EFCC ta gayyata kan kudin sun hada da Misis Esther Nenadi Usman da tsohuwar Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje Farfesa biola Onwilari.