✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Baga a matsayin zakaran gwajin dafi ga sojoji

Wannan gari na Najeriya da ke kusa da Tafkin Chadi a shekaru da dama ya kasance hedkwatar sojin hadin gwiwa (MNJTF) da suka fito daga…

Wannan gari na Najeriya da ke kusa da Tafkin Chadi a shekaru da dama ya kasance hedkwatar sojin hadin gwiwa (MNJTF) da suka fito daga kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, kuma ana sa ran su sanya aya ga mayakan Boko Haram.

Sai dai a wata fafatawa da aka shafi wuni kamar yadda bayanai da dama suka nuna, mayakan da ake zargin a makon jiya sun kwace Baga, wani garin masunta da sananne ne wajen samar da kudin shiga ga Jihar Borno, inda suka fatattaki sojojin hadin gwiwar na MNJTF.
Kan wasu dalilai da ba a sani ba, bayanai sun ce an janye sojojin kasashen Nijar da Kamaru da Chadi zuwa kasashensu ’yan awanni kafin maharan su kai farmaki. Kakakin Hedkwatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade ya fadi a wata sanarwa cewa bayyana farmakin a “matsayin mafi muni” a rikicin na shekara shida da aka ce ya lashe rayukan dubu 13 tun shekarar 2009 “hakika gaskiya ne.”
An ba da rahoton cewa maharan sun kafa tutarsu a hedkwatar MNJTF sannan sukayi gaba suna lalata kauyukan da ke kusa, ya nuna alkawuran da Shugaba Goodluck Jonathan da manyan hafsoshin sojansa suka rika yi cewa za su fatattaki maharan daga garuruwan da suka kwace a hare-haren baya zance banza ne.
Mazauna Baga sun gudu zuwa Chadi ta keta ruwa Tafkin Chadi, yayin da saura suka nufi Kudu zuwa sassan Jihar Borno don tsira da rayukansu. Rahotanni game da rayukan da aka rasa sun kama daga fararen hula 2000 zuwa daruruwa; kuma an kashe sojoji da dama a harin. Gidaje da shaguna da motoci da kayan amfanin gona da gine-ginen gwamnati da dama duk maharan sun kone su. Idan za a tuna wannann ne karo na biyu da mazauna garin Baga suka hadu da irin wannan mummunan lamari, na farko shi ne na ranar 23 ga Afrilun bara, inda aka kashe kimanin mazaunansa 200, ciki har da mata da yara.
Wani jami’in karamar Hukumar Kukawa, Musa Usman, wanda y ace shi ganau ne a fafatawar da aka yi, ya ce maharan sun kai hari Baga ne cikin ayarin akori-kura dauke da bama-bamai da kuma tankokin soja. A cewar Usman, a fili yake wasu daga cikin maharan ba su jin harsunan mutanen gari wato Kanuri da Shuwa Arab ko Hausa. Ya ce sojojin sun fafata da maharan na wasu awanni, sannan suka janye, mai yiwuwa saboda dabarun yaki.
Sojojin da ke fagen-daga dai sun yi ta korafi kan rashin ingantattun kayan aiki da za su tunkari abokan gaba, wadanda suka suka tashi daga yakin sari-ka-noke zuwa fafatawa ta gaba-da-gaba. Rundunar soja ta sha karyata cewa sojojin ba su da makamai. Amma me zai sa kwararrun sojoji su kaurace wa fafatawar gaba-da-gaba idan ba an fi su kayan yaki da karfafa musu gwiwa ba.
Wajibi ne hukumomin soja su yi duk abin da ya wajaba wajen sake farfado da karfin gwiwa da jarumta da karfin hali da kishin kasa ga sojoji, domin a samu nasarar yaki da wadannan mahara masu zubar da jini. Abin damuwa ne a ce garin Baga da ke daya daga cikin garuruwan da aka kwace daga ’yan Boko Haram ya sake fadawa hannunsu. Abu mafi bata rai, shi ne wannan mummunan lamari an tsara shi ne a daidai lokacin da saura ’yan makonni a gudanar da zaben kasa. Wajibi ne hukumomin soja su bullo da dabaru da daman a kwato garuruwan da aka kwace tare da samun nasara a kan maharan. Duk lokacin da aka kwato wani yanki na kasa daga maharan, gwamnati ta hannun hukumominta ta tabbatar wa mazauna wadannan yankuna ba a fatar baki kawai ba a aikaci cewa za a kare rayuka da dukiyarsu. Wajibi ne a kokari wajen sake gina garuruwan da aka lalata, ciki har da gine-ginen gwamnati da suka hada da makarantu da asibitoci ta yadda mazaunansu za su koma su ci gaba da rayuwa yadda suka saba.
Wajibi hukumomin soja su hana sake faruwar irin abin da ya faru da Baga su hana maharan wani yunkuri na rikewa ko ci gaba da karfafa ikonsu da kowane yanki. Janye sojoji da wasu makwabta kasashen da suka tallafa da sojojin hadin gwiwa na MNJTF, lamari ne da ke bukatar Gwamnatin Tarayya ta samo amsar abin da ya jawo haka.
Wannan ya zama wajibi ne idan aka lura da cewa maharan barazana ne ga daukacin kasashen yankin. Rasa Baga ya kamata ya zama zakaran gwajin dafi ga hukumomin soja na su sake kwato kowane taku daya da ke hannun maharan a yanzu.