✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Basarake mai shekaru 116 ya rasu a jihar Kogi

Wani basarake mai sarautar Obobanyi a masarautar Ohionwa a lardin Ihima, da ke karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi, mai suna  Jeremiah Akaava, ya rasu…

Wani basarake mai sarautar Obobanyi a masarautar Ohionwa a lardin Ihima, da ke karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi, mai suna  Jeremiah Akaava, ya rasu a daren jiya Juma’a ya nada shekaru 116.

A wata sanarwa da masarautar  Ohionwa ta fitar yau Asabar a Lokoja ta ce, basaraken ya rasu ne a jiya Juma’a da daddare.

Sanarwar na bayyana cewa, basaraken ya rasu ne yana rike da sarautar shekaru 36 da yi masa rawani, kamar yadda daya daga cikin ‘yan masarautar Mista Yusuf Itopa ya sanar a madadin masarautar Ohionwa.

Yusuf Itopa, ya bayyana Marigayin a matsayin mutum mai san zaman lafiya da hadin kan ‘yan masarautar da jihar Kogi da ma Najeriya baki daya.