✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batutuwan dubawa game da ’yan sandan yanki

A da can shekarun baya, ’yan doka (’yan sandan yanki) ne ke kula da al’amuran tsaro a yankuna da sassan Najeriya. Wato a wancan lokacin,…

A da can shekarun baya, ’yan doka (’yan sandan yanki) ne ke kula da al’amuran tsaro a yankuna da sassan Najeriya. Wato a wancan lokacin, babu Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF), kuma wadannan jami’an ’yan doka suna gudanar da ayyukansu da inganci fiye da jami’an ’yan sandan kasa na yanzu, ta yadda zaman lafiya da kwanciyar hankali ke gudana a ko’ina.

An kafa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ne bayan da kasar nan ta koma Tsarin Mulkin Tarayya, ta yadda aka dauki jami’an ’yan sanda daga ko’ina na sassan Najeriya. Ga shi yanzu saboda al’amuran tsaro sun tabarbare, manya da kananan laifuka sai ta’azzara suke yi a karkashin wannan tsari na ’yan sandan kasa. Ni a ganina, lokaci ya yi da ya kamata a koma wa tsarin baya, inda kowane yanki zai kafa rundunar ’yan sandansa, wadanda za su kula da al’amuran tsaron yankunansu.

A lura, ni ina son a kafa rundunar ’yan sandan yankuna ne, ba ’yan sandan jiha ba, domin kuwa wasu za su ga cewa, idan aka ce ‘jiha’ ana ganin gwamnoni za su iya amfani da karfin mulkinsu, su juya su zuwa amfanin kansu, maimakon al’umma. Idan kuwa aka kafa na yanki, ina ganin abin zai fi yin tasiri, domin kuwa jami’an yankin su suka fi sanin sirrin yankunansu, ta yadda za su iya magance kowace irin matsala da za ta taso ta fuskar tsaro, maimakon baki. 

Ba zan taba mancewa ba, a shekarun 1950 zuwa 1960, lokacin ina makarantar firamare, na lura da yadda jami’an ’yan doka suke gudanar da aikinsu cikin da’a da kishin kasa. Jami’an, suna aikinsu ne bisa kauna da kishin al’umma, ganin cewa yankinsu ne kuma al’ummarsu ce suke wa aiki. Haka kuma, jami’an za ka ga suna tsoma kansu cikin aiki wurjanjan, musamman ma idan wata masifa kamar gobara ta tashi. Za ka same su suna aikin kashe gobarar tare da sauran al’umma cikin nuna kishin al’umma a zukatansu.

Wani abin lura kuma shi ne, gudanar da rundunar ’yan sandan yanki tana da rahusa, musamman saboda babu bukatar gina bariki, kasancewar kowane jami’i yana zaune a garinsu ne, cikin al’ummarsa. Wannan kuma zai ba shi damar sanin duk wani abu da ke faruwa a yankinsa, ta yadda da zarar an samu labarin wani mugun bako ko wani mai nufin tada hankali, cikin lokaci za a magance kudurinsa.

Babu shakka, kamar yadda zan iya tunawa, akwai zaman lafiya sosai a wancan zamanin, duk da cewa ana samun kananan barayi nan da can, kamar kuma yadda a wasu lokutan ake samun ’yan fashi da makami, wanda cikin lokaci asirinsu ke tonuwa, ’yan doka ke dakile hanzarinsu. A wancan lokacin, akawi wani gagararren dan fashi a yankinmu, mai suna Malam Gulani. Yakan yi fashi kamar irin yadda Robin Hood yake yi, amma daga bisani ’yan doka suka gano mabuyarsa, suka kama shi, suka raba al’umma da ja’ibarsa.

Wannan ingantaccen aiki na kare lafiya da dukiyar al’umma ya faru ne a can shekarun baya, yadda ’yan doka suka rika aiki wurjanjan, suna dakile ayyyukan mabarnata cikin izza da jaruntaka. Haka suka rika aiki har zuwa shekarar 1972, inda aka kirikiri Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF). Sannu-sannu sai aka yi ta karkasa ta zuwa shiyyoyi, jihohi da kuma yankunan kananan hukumomi. Har yanzu wannan tsari ne ke gudana, amma abin tambaya a nan shi ne, wannan tsari yana da tasiri ga al’umma kuwa?

A yau da tashe-tashen hankula da aikata laifuka suka zama ruwan dare a Najeriya, mutane na ta neman a duba yanayin aikin ’yan sanda a kasar nan. An ba da shawarar a kafa rundunonin ’yan sanda na jihohi. Bisa ga wannan koke, a kwanakin baya da Shugaban kasa ya ziyarci Jihar Kwara, ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa Ta kasa ta nuna cewa a bar wannan batu har sai lokacin da kan al’umma ya ida wayewa, ta yadda tsarin zai yi tasiri. Kwanakin baya ma Gwamnan Jihar Yobe ya ce a taronsu na kungiyar Gwamnonin Najeriya, gwamnoni biyu ne kadai suka amince da batun. Wannan kuwa abin mamaki ne da gwamnonin suka ki amincewa da wannan batu.

Ni kuwa a nawa ra’ayin, akwai bukatar a sake duba yadda ake gudanar da al’amuran tsaro a kasar nan, musamman ma ta fuskar aikin ’yan sanda. Ga shi dai al’umma sai karuwa take, don haka akwai wahala tsarin da ake gudanarwa na aikin ’yan sanda ya zama mai tasiri. Wannan tsari da ake ciki na ’yan sandan tarayya, yana haifar da rige-rigen samun mukami ne kawai a tsakanin jami’an, sannan kuma ga tsadar gudanarwa. Don haka, kamata ya yi a kirkiri rundunonin ’yan sanda na yanki-yanki, kamar yadda yake a can baya.

Wadanda ke kin wannan batu na ’yan sandan yanki, suna tsoron kada ’yan siyasa su rika amfani da jami’an ne wajen biyan bukatunsu na siyasa, kamar kuma yadda shugabannin ’yan sanda na yanzu ke ganin za a rage musu martaba da girma ne idan tsarin ya canza zuwa na yankuna. Ni kuwa ina ganin wadannan ba su isa dalilai na kwarai ba, domin kuwa hatta yadda wasu kungiyoyi ke mallakar makamai a yankuna, suna tada hankali, idan wannan tsarin ake gudanarwa, za a iya maganinsu cikin sauri.

Lallai ne akwai tsananin bukatar a jaraba wannan tsari na rundunar ’yan sandan yanki, musamman idan aka inganta tsarin yadda zai dace da wannan zamani da ake da wadatar na’urori. Mafi yawan matsalolin da ake fuskanta a furkar tsaro a wannan zamani sun dogara ne da cewa, mafi yawan jam’ian ’yan sanda baki ne a yankunan da suke aiki. Da a ce jami’an haifaffun yankunan da suke aiki ne, da za su iya gudanar da aikinsu cikin sauki da inganci, ganin cewa suna da masaniyar lunguna da sako-sakon yankunansu. Idan aka kirikro su, sai kuma a tanadar musu da ingantattun kayan aiki na zamani, wanda haka zai tallafa masu su gudanar da aikinsu cikin kwarewa da inganci.

Masu tsoron cewa wai ’yan siyasa na iya amfani da ’yan sandan yankin wajen cin ma manufofinsu, ai ko a wannan tsarin ma ana amfani da jami’an tsaro a siyasance. Domin kuwa ga EFCC nan ma, wacce ta Gwamnati Tarayya ce, amma a shekarun baya aka samu cewa ta hada baki da wasu ’yan majalisar jihohi, suka tsige gwamna! Babu abin da zai maganin irin wannan sai gaskiya da amana daga bangaren shugabanni. Don haka, lallai ne a maida hankali wajen kirkiro rundunonin ’yan sandan yanki, musamman a yanzu da ake batun sake fasalin tsarin mulki.

Ba tare da bata lokaci ba, lallai ne a tanadar da dokar da za ta ba jihohi ikon kafa rundunar ’yan sanda, tare da tanadar musu da sharidodi da dokoki masu inganci, ta yadda duk wanda ya saba wadannan ka’idoji wajen gudanarwa da tafiyar da rundunar, sai a janye izinin. Ke nan ita Gwamnatin Tarayya za ta zama mai kula da yadda ake tafiyar da rundunonin, ta yadda ba za a saba ka’idar tafiyar da su ba. Haka kuma, ya zamanto majalisun kasa za su iya amsar rahotannin yadda ake tafiyar da rundunonin daga lokaci zuwa lokaci, duk dai domin kada a samu sabani ko karya tsarin. Karin maganar nan da ke cewa wukar nesa ba ta iya taimako, gaskiya ne. Al’ummar yanki su suka san abin da ke faruwa a yankunansu, don haka ’yan sandan da aka dauka aiki a yankin, su za su fi aiwatar da aikinsu cikin inganci da biyan bukata fiye da na nesa. Ga shi kuma tsarin zai kasance mai sauki da rahusar gudanarwa. Lallai ne a jaraba kirkiro wannan runduna ta ’yan sandan yanki a yanzu, domin a ceci al’ummar da wasu karkatattun miyagu ke cuta a kullum.