✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Biyafara bankaura ce’

A ranar Litinin da ta gabata ne Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi masu zanga-zangar fafutikar kafa Jamhuriyyar Biyafara, inda ta ce tura ta kai bango…

A ranar Litinin da ta gabata ne Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi masu zanga-zangar fafutikar kafa Jamhuriyyar Biyafara, inda ta ce tura ta kai bango kuma a shirye take ta dakile duk wata barazana kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya ba ta dama, tare da kare martabar kasar nan da kuma tabbatar da hadin kanta.

Gargadin ya fito ne daga bakin Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Runduna ta 82 da ke Jihar Enugu, Kanar Hamza Gambo, inda ya ce ci gaba da jerin zanga-zanga da wasu masu neman kafa kasar Biyafara suke yi a yankin Kudu maso Gabas da kuma wani bangare na Kudu maso Kudu yana barazana ga tsaron yankin.
Ya ce duk da cewa masu zanga-zangar kamar sauran ’yan Najeriya suna da ’yancin bayyana ra’ayinsu da kuma gudanar da taruka cikin lumana, amma hakan ba ya nufin suna da damar taka ’yancin wasu. Ya ce ba za su kawar da idonsu daga nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu na dakile duk wata barazanar tayar da kayar baya ba da zarar an bukaci su taka wa masu zanga-zangar birki.
Hakazalika Ministan Tsaro Birgediya Janar Mansur dan-Ali (mai ritaya) ya ce idan aka zura wa masu zanga-zangar ido abin zai iya tabarbarewa ya zama wata babban barazanar ga kasancewar kasar nan dunkulalliyar kasa. Sai ya bukaci Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a batun su tattauna domin lalubo hanyar warware matsalar saboda kauce wa rugujewar kasar nan.

’Yan Najeriya sun fi so zama a dunkule – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya la’anci hare-haren da masu neman ballewa don kafa kasar Biyarafa suka kai, inda ya ce Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa tun lokacin samun ’yancin kai.
Jawabin na Shugaba Buhari ya zo ne a daidai lokacin da zanga-zangar neman kasar Biyafara ke dada azazzala a sassan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, inda masu zanga-zangar ke neman a sako Nnamdi Kanu daraktan gidan rediyon Biyafara wanda ke tsare tun cikin watan jiya.
Shugaba Buhari wanda ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata a dakin taro na Fadar Shugaban kasa da ke Abuja lokacin kaddamar da Gidauniyar Tunawa da Tsofaffin Sojoji ta shekarar 2016, ya ce tun samun ’yancin kai ’yan Najeriya suke zaune cikin hadin kai, kuma sun yanke shawarar ci gaba da zama a dunkule a kasar nan fiye da baya.
“Kwanan nan kasarmu ta yi bikin cika shekara 55 da samun ’yanci da kuma ci gaba da zama dunkulalliyar kasa duk da manyan matsalolin da ta fuskanta. Najeriya ta hadu da matsalolin tashin tashina a cikin gida tun samun ’yancin kai, ta tsallake Yakin Basasa kuma ta ci gaba da kasancewa a dunkule. Wannan nasara da aka samu wata manuniya ce kan kudirin ’yan Najeriya na kasancewa al’umma daya,” inji Shugaba Buhari.

Akpabio da ACF sun la’anci tarzomar masu neman kasar Biyafara
Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom kuma Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya yi Allah wadai ne da masu zanga-zangar, inda ya bukaci iyaye da shugabannin al’umma a yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu su ja kunnen ’ya’yansu a kan abin da ka je ya zo.
Tsohon Gwamnan ya yi bayanin ne lokacin da ’yan majalisar Jihar Akwa Ibom suka kai masa ziyara a Abuja a ranar Alhamis din makon jiya. Ya ce: “Mu da aka yi yakin basasa a kan idonmu, ba za mu goyi bayan wannan yunkuri ba, saboda abu ne da babu alamun nasara da kuma alheri a cikinsa. Kowane matsayi kake takama da shi ko kuma a wace jam’iyya kake goyon baya ba alheri ba ne. Duk yadda wasu jama’a suke ganin an yi musu ba daidai ba, akwai hanyoyi da doka ta tanada don neman hakki. Ya kamata dukkanmu mu tashi da murya guda don yin Allah-wadai da duk wasu masu burin rusa kasancewarmu kasa daya, saboda hadin kanmu shi ne tasirinmu.”
Sanata Akpabio ya bukaci dukkan ’yan Najeriya su kasance tsintsiya madaurinki daya, inda ya ce hadin kai ne kawai zai sa kasar nan ta samu ci gaban da ake fata. “Mu manta da duk wasu bambance- bambance. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana bukatar zaman lafiya don ci gaba mai dorewa kuma hakan zai tabbata ne kawai idan ya samu natsuwa,” inji shi.
kungiyar ACF ta bukaci ’yan kungiyar MASSOB da ke yankin Kudu maso Gabas su kauce wa duk wani abu da ka iya janyo rikici domin batun neman kasar Biyafara tuni aka binne shi.
ACF ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a kan zanga-zangar da ’yan MASSOB ke yi da kuma zargin kai wa ’yan Arewa hari da ’yan MASSOB din suka yi a tashar Elelenwa da ke a garin Fatakwal ta Jihar Ribas a makon jiya.
ACF ta yi Allah wadai da wannan yunkuri da kuma harin da aka kai wa ’yan Arewa a yankin, kamar yadda sanarwar dauke da sa hannun Kakakin ACF, Muhammad Ibrahim ya fitar, inda ta ce abin da ’yan MASSOB din suka yi a garin Fatakwal abin bakin ciki ne.
“kungiyar ACF ta samu bayanin cewa ’yan ta’addan MASSOB sun nemi tada hankulan ’yan Arewa da ke kasuwancinsu a kasuwar dabbobi da ke Elelenwa a Fatakwal, inda suka lalata shaguna da dukiyoyin ’yan Arewa. Amma dai taimakon da jami’an tsaro suka kai wajen ya sa an kare yaduwar lamarin. Wannan abin bakin ciki ne matuka, idan aka yi la’akari da irin matsifar da hakan ka iya janyo wa kasar nan,” inji sanarwar.
Ta kara da cewa: “’Yan ta’addan MASSOB masu zanga-zanga sun dade suna neman tada fitina a yankin Kudu maso Gabas da sunan neman ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafara wanda kuma hakan ba zai yiwu ba. Najariya ta dandana Yakin Basasa shekara 45 da suka wuce domin kare martabar kasar nan, tuni aka kashe wannan batu na neman kafa kasar Biyafara aka kuma binne zancen. Saboda haka Najeriya ba za ta taba yarda da wani Yakin Basasa ba a wannan lokaci da kowa ke kokarin ganin an ciyar da kasar nan gaba.”
ACF ta kara da cewa: “Bai dace a kawar da hankalin Gwamnatin Tarayya ke yi ba, na kawo karshen ’yan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas a wannan lokaci ba. Kuma ACF ta yaba wa kokarin jami’an tsaro da gwamnatin Jihar Ribas wajen dakatar da rikicin na tashar Elelenwa tare da maido da zaman lafiya a yankin.”
“Saboda haka ACF na kira ga ’yan MASSOB, musamman matasan yakin Kudu maso Gabas wadanda mafi yawansu ba a haife su ba a lokacin da aka yi Yakin Basasa a yakin, da su mika kokensu zuwa ga ’yan majalisunsu tunda mulkin dimukuradiyya ake yi. Kuma su saurari shawarwarin da gwamnoninsu da shugabannin Ibo da suka fito fili suka yi Allah wadai da wannan yunkuri na matasan,” inji ACF.
Sai ACF ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dauki dukkan matakan da suka kamata wajen kawo karshen duk wani mai neman tada zaune tsaye a kasar nan.

Aiki ne na shaidanci – Rabaran Mbaka
A ranar Asabar da ta gabata ma Bishop din Cocin Katolika a Enugu wanda ya taba nuna adawarsa a fili ga tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Rabaran Ejike Mbaka, ya yi Allah-wadai da masu zanga-zangar inda a cikin hudubarsa ya bayyana aikin nasu da cewa wani aiki ne na shaidanci.
Rabaran Mbaka ya yi kira ga matasa a yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu su kaurace wa zanga-zangar saboda za ta iya zama ajalinsu.
“Rufe shaguna da dakatar da harkokin kasuwanci ba za su kara musu Naira daya a aljihunsu ba, duk wani korafi da suke da shi za a iya warware shi ta hanyar sulhu,”inji shi.
Daga nan ya soki shugabannin da suke ingiza masu zanga-zangar, inda ya bukaci su fara tura ’ya’yansu su yi zanga-zangar.
Rabaran Mbaka ya yaba wa Shugaba Buhari saboda yadda ya zabi wasu ministocinsa daga yankin kuma ya ba su manyan ma’aikatu. “Shugaba Buhari ya tabbatar mana cewa ba zai danne yankin Kudu maso Gabas ba. Zan fito in yi magana idan da a ce bai nada kowa daga yankin nan ba,” inji shi.
Ya dora alhakin tabarbarewar al’amura a yankin a kan shugabannin kabilar, inda ya ce tsofaffin gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya sun kasa sauke nauyin da aka dora musu. Ya ce: “Shugaba Buhari ba shi ne sanadiyyar lalacewar hanyoyinmu da matsalar rashin aikin yi da kuma lalacewar abubuwan more rayuwa a yankin ba. Mun dora wannan laifin ga shugabanninmu. Yawancin hanyoyinmu an bayar da kwangilarsu, amma shugabanninmu sun yi sama da fadi da su kuma ba su ko damuwa.”
Daga nan ya yi kira ga sabon Ministan kwadago da Samar da Ayyuka, Sanata Chris Ngige ya yi amfani da ofishinsa wajen samar wa matasan yankin aikin yi. Ya ce hakan ne zai sa a kauce wa wani rikicin Boko Haram a yankin Kudu maso Gabas.
Kuma ya yaba kan yakin da Shugaba Buhari ke yi da cin hanci da rashawa, ya ce hakan ne zai tabbatar da ka’ida da kuma tsafta wajen shugabanci. Sai ya bukaci ’yan Najeriya su yi hakuri da shugaban saboda yadda yake da kyawawan manufofin ciyar da kasar nan gaba.

Yi wa kabilar Ibo kafar ungulu ne a shekarar 2023 – APC
Shiyyar Kudu maso Gabas na Jam’iyyar APC ta ce zanga-zangar neman kasar Biyafara da wasu ke yi a yankin na iya kawo cikas ga damar da ’yan kabilar Ibo suke da ita ta samar da Shugaban kasa a shekarar 2023, inda ta bukaci masu zanga-zangar su daina.
Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a shiyyar Osita Okechukwu ya fitar a farkon wannan mako ya ce jam’iyyar ta lura gwagwarmayar kungiyar Tabattar da ’Yancin kasar Biyafara (MASSOB) da ta Al’ummar ‘’Yan Asalin Biyafara (IPOB) na iya jawo cikas ga bukatar al’ummar Ibo na samar da Shugaban kasa a shekarar 2023.
Sanarwar ta kara da cewa: “Yayin da muka amince cewa akwai dimbin rashin aikin yi da zaman kasha wando a tsakanin matasan kasar nan, amma wannan bay a takaita a Kudu maso Gabas kawai ba ne. Rashin aikin yi matsala ce da ta shafi kasa kuma za a magance ta, abin farin ciki danmu Sanata Chris Ngige ne