✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cinikin akwatin gawa na habaka a Pakistan

Masu kera makara da akwatin gawa a Yankin Arewacin kasar Pakistan na samun makudan kudi, a sanadiyyar rowan bama-bamai da ke yi wa birnin Pashawar…

Masu kera makara da akwatin gawa a Yankin Arewacin kasar Pakistan na samun makudan kudi, a sanadiyyar rowan bama-bamai da ke yi wa birnin Pashawar kusan kullum, kamar yadda Kamfnain Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.

Akwatin gawa bay a cikin al’adun Musulunci na alkinta gawa, musamman a kasar Pakistan, inda ake lullube gawa da likkafani, a dora a makara, a yi mata sallar jana’iza, sannan a binneta.
Sai dai a halin yanzu ana samun wadanda harsashin bindiga da bom da nakiya suka yi kaca-kaca da jikkinsu, irin wadannan gawarwakin akan tattara sassan jikinsu a akwati.
Jehanzeb Khan, wani dattijo dan shekara 60, shi ya fara kera irin wannan akwati
”Nakan sayar da akwatuna biyu zuwa uku a farkon sa’adda na fara kasuwancina,” in ji Khan, wanda ya fara kera wannan sana’a ta kera akwatin gawa, tun cikin shekarun 1980, kamar yadda ya bayyana a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
A da abokan huldar cinikinsa, mafi yawansu ’yan gudun hijira ne daga kasar Afghanistan, wadanda kasar Rasha ta mamaye kasarsu, inda suke sayen akwatin da su kai gawarwakinsu gida don binnewa; ko kuma iyalan da ke bukatar hatta gawar matansu su kasance cikin kulle, don haka suke kawar da su daga idon mazan da ba su jibance su ba, ta hanyar kulle gawarsu a cikin akwati.
Wannan ciniki na akwatin gawa ya fara samun habaka tun daga shekarun 2004.
Gwamnatin Pakistan ta bayyana cewa, an yi asarar rayuka sama da dubu 50, a sanadiyyar harsashin bindiga da bom da hare-haren kunar bakin wake. Kuma masu kera akwatin gawa sai kokari suke yi wajen ganin sun cika alkawari ga abokan ciniki da ke bukatar kayan.
A halin yanzu akwai masu gasa da Khan a wannan sana’a, wadand ayawansu ya kai 40, tare da sauran masu sana’ar da ke kewayen wannan birni, mai yawan mutanen da suka kai miliyan hudu d arabi, kuma suna sayar da a kalla 15 a kowace rana.
“Mutane sun fara ganin akwatin gaw ane a asibiti, amma yanzu har wadanda suka mutu salun-alun a gidajensu akan saya musu akwatin,” inji Khan.
Ya ce yana kokarin kera akalla guda 80, wadanda za a ajiye su, musamman ma in an yi la’akari da hare-haren ’yan Taliban na watan da ya wuce, a wata makaranta da ke Pashewar, inda akalla mutum 150, wadanda mafi yawansu kananan yara ne suka rasa rayukansu. A wannan harin kantin Khan ya samu abokan ciniki da suka bukaci ya kera musu akwatunan gawa 60.
Shi kuwa, wani matashi dan shekara 23, Shehryar Khan ya fi yi wa sojoji da jami’an tsaro kwatunan gawa, musamman wadanda hari ya rutsa da su.
“Muna yi wa sojoji akwatunan gawa. Sun fi son a yi amfani da kayan aiki masu nagarta, musamman katako da marikin akwatin,” a cewar Khan, inda ya bayyana cewa akwati mara tsada bai wuce a saye shi kan Dala 30 (Naira dubu shida), shi kuwa mai tsadar yakan kai Dala 100, wato daidai da Naira Dubu 20.
Yawan bukata ta sanya Shehryar Khan ke sanya ma’aikata masu aiki a kodayaushe.
“A cikin shago nike kwana,” a cewar mai sayar da kayan, Niaz Ali Shah, kamar yadda ya bayyana a hirar da ya yi da Kamfnain Dillancin Labarai na AFP.