✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dokar ta-baci ba ta amfani Yobe da komai ba’

Shugaban Rundunar Adalci ta kasa reshen Jihar Yobe Malam Zakari Adamu ya ce dokar ta-baci da Gwamnatin Tarayya ta kafa a jihohin Borno da Yobe…

Shugaban Rundunar Adalci ta kasa reshen Jihar Yobe Malam Zakari Adamu ya ce dokar ta-baci da Gwamnatin Tarayya ta kafa a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da wa’adinta zai cika a wannan wata ba ta da wani amfani asali ma kara rikita al’amura ta yi maimakon inganta su, inda harkokin tsaro suka sake rincabewa musamman a Jihar Yobe.

Malam Zakari Adamu ya bayyana haka ne a tattaunwarsa da Aminiya dangane da tasirin dokar da abin da ta haifar, inda ya ce kafin gwamnatin ta kafa dokar a Jihar Yobe a watan Mayun bana harkokin tsaro sun fara inganta a duk fadin jihar, “to amma bayan kafa dokar sai abin ya zama gara jiya da yau,” inji shi.
Malam Zakari ya ce, bayan kafa dokar ce aka samu mugayen hare-haren da suka haddasa rasa rayuka masu yawa musamman na dalibai da malamai a makarantun sakandaren Damaturu da Mamudo da Kwalejin Nazarin Aikin Gona ta Gujba da kuma hare-haren baya-bayan nan na garin Damaturu da sauransu, “amma duk da dimbin jami’an tsaron da ake da su a jihar da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ke kansu sun gaza yin wani abin a zo a gani,” inji shugaban.
Don haka ya roki Gwamnatin Tarayya da kada ta kara koda kwana daya da zarar wa’adin dokar, “A bar al’umma su ji da abu daya alabarshi su ci gaba da hana idanuwansu barci ta wajen dukufa da addu’ar Allah Ya kawo karshen wannan lamari.
Ya ce babban abin bakin ciki shi ne yadda gwamnatin Jihar Yobe ke ci gaba da zakewa wajen fitar da makudan kudi a kan harkokin tsaro da ake fakewa da haka wajen yin wa-ka-ci-ka-tashi da dukiyar jama’a alhali duk manyan jihar sun kwashe iyalansa zuwa wajen jihar.
Shugaban ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta jihar su gaggauta kawo dauki ga al’ummar jihar don fitar da su daga kuncin rayuwa ta hanyar samar musu abinci da aikin yi da jari ga ’yan kasuwar da suka karye. “Yadda akasarin al’ummar jihar ke rayuwa a yanzu babban abin damuwa ne, jama’a da yawa sun zama mabaratan dole, za ka rika ganin mata da yara da magidanta a kan tituna suna barar abin da za su ci, ga zaurawa da marayu sun yawaita sakamakon mutuwar jagororin gidajensu,” inji shi.