✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duba-gari sun kai ziyarar ba–zata ga mayankar Abuja

Jami’an kula da tsabta (duba-gari) sun kai ziyarar ba-zata ga mayankar Abuja da ke hanyar Kubwa zuwa Zuba inda suka iske ana babbaki fatun dabbobi…

Jami’an kula da tsabta (duba-gari) sun kai ziyarar ba-zata ga mayankar Abuja da ke hanyar Kubwa zuwa Zuba inda suka iske ana babbaki fatun dabbobi da ta hanyar kone su da tayoyin mota.
Yin kicibis da hayakin da ke turneke sararin samaniya a kan hanyar Kubwa zuwa Zuba a yankin Birnin Tarayya, Abuja musamman a tsakanin karfe 6:00 zuwa 11:00 na safe, ba sabon abu ba ne ga masu zirga-zirga a kan titin, sai dai ga sababbin masu bin hanyar na iya daukar hayakin a matsayin na gobara ko wani hadari da ke shirin ruwa.
Masu babbaka a mayankar ta Abuja da ke cikin babbar kasuwar dabbobi ta Abuja da ke Deidei da tsofaffin tayoyi da robobi a wajen babbakar awaki da fatu da kafofin shanu, kuma hayakin tayoyin da robobin ne ke mamaye sararin samaniyar yankin.
Aminiya ta samu labarin cewa al’amarin yana jawo kunci ga masu gudanar sauran harkoki kasuwar da mazauna yankin sakamakon yadda hayakin tayoyi da robobin ke bakanta gine-gine da bata suturar jama’a a tsawon lokacin aikin na u, baya ga illarsa ga lafiya da masana kiwon lafiya da aka tuntuba suka ce zai iya yi.
Wata majiya a Sakatariyar Kula da Noma da Raya Karkara a Ma’aikatar Birnin Tarayya da kasuwar ke karkashinta, ta ce kai samamen da dubagarin suka yi daga ofishin nasu, ya biyo bayan korafe-korafe ne daga jama’a, amma ba tare da daukar wani mataki ba sai a wannan karo, sakamakon nade-nade da sauyin wuraren aiki ga wasu jami’an sashin.
A yayin samamen duba-garin wadanda suka samu rakiyar jami’an tsaro na Sibil Difens, sun kwace tarin tayoyi da robobi daga wurin mahautan suka lalata su a harabar ofishinsu na cikin kasuwar.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin sabon Manajan Kasuwar bai samu nasara ba, sai dai wata majiya a Sakatariyar Birnin Tarayya ta ce tuni hukumar ta shiga wata yarjejeniya a tsakaninta da wata cibiya da ke birnin Kano don ta kirkiro wani risho da ke yin amfani da gawayi wajen yin babbaka wanda aka bayyana shi da mai sauki gudanarwa da cibiyar za ta sayarwa mahautan kai-tsaye.
Haka wasu dalibai masu yawon bude ido ’yan kasar Jamus da suka ziyarci wajen babbakar bayan samun izini daga sakatariyar, sun ba da gudumawar kayayyakin aiki ga mahautan da suka hada da dogayen riguna don rage musu zafin wuta da takalman ruwa da abin rufe baki da hanci.
A yanzu haka dai an tilasta wa mahautan amfani da itace ko katako wajen yin babbakar, sai dai bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa har yanzu wasu daga cikin mahautan suna amfani da robobi wajen yin babbakar idan dare ya raba.