✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar addu’a

Wani Banufe ne yake ta rokon Allah a dakin Ka’aba, sai wani Bahadeje da ke kusa da shi, shi ma ya daga hannu yana rokon…

Wani Banufe ne yake ta rokon Allah a dakin Ka’aba, sai wani Bahadeje da ke kusa da shi, shi ma ya daga hannu yana rokon Allah yana cewa: “Ya Allah, duk abin da ka ba Banufen nan, ka ba ni irinsa ninki biyu.”
Ko da Banufen nan ya ji haka, sai ya ce: “Ya Allah Ka sa idona daya ya nakasa.” Ke nan idan ido daya na Banufe ya mutu, shi Bahadeje zai rasa nasa idanun biyu duka.
Daga Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi, 08095968366