✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Zakarun Turai

Dinamo Zagreb ta doke Arsenal 2-1*Jubentus ta yi wa Man City 2-1 a gida kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke kasar Ingila ta sha…

Dinamo Zagreb ta doke Arsenal 2-1*Jubentus ta yi wa Man City 2-1 a gida

kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke kasar Ingila ta sha kashi a hannun takwararta ta Dinamo Zagreb da ci 2-1 a gasar cin Kofin Zakarun Turai da suka kara a shekaranjiya Laraba.
Dinamo ta fara cin kwallon farko ne a minti na 24 da fara wasan, bayan da Odlade-Chamberlain ya ci gida, sannan ta kara ta biyu ta hannun Junior Fernandes.
Sai dai kungiyar Arsenal ta farke kwallo daya ta hannun Theo Walcott saura minti 11 a tashi daga wasan.
kungiyar Arsenal ta karasa wasan da ’yan kwallo 10 a fili, bayan da aka bai wa Olibier Giroud jan kati saboda ketar da ya yi wa Ibo Pinto.
A karawa ta biyu ta gasar Arsenal za ta karbi bakuncin Olympiacos ta Girka a ranar Talata 29 ga watan Satumba a filin wasa na Emirates da ke birnin Landan.
A wasan da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta buga ita ma ta sha kashi a hannun a hannun Jubentus ta kasar Italiya a gasar ta cin Kofin Zakarun Turai da suka buga a filin wasa na Ettihad a ranar Tatata.
Manchester City ce ta fara zura kwallo ta hannun Kyaftin dinta bincent Kompany a minti na 12 da dawowa daga hutun rabin lokaci.
Sai dai Jubentus ta farke kwallon ta hannun Mario Mandzukic, sannan Albaro Morata ya kara ta biyu a ragar City saura minti tara a tashi daga wasan.