✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisba a Jigawa ta tarwatsa bikin masu auren jinsi

Rundunar Hisba ta Jihar Jigawa ta tarwatsa gungun ’yan daudu a kauyan Kadume da ke karamar Hukumar Jahun a ranar Asabar da ta gabata, a…

Rundunar Hisba ta Jihar Jigawa ta tarwatsa gungun ’yan daudu a kauyan Kadume da ke karamar Hukumar Jahun a ranar Asabar da ta gabata, a daidai lokacin da suke kokarin yin bikin auren ’yar tsana, wato bikin auren jinsi (namiji ya auri namiji).

Kamar yadda mukaddashin shugaban rundunar ta Hisba, Malam Ibrahim Dashiru Garki ya ce, masu bikin auren jinsin sun fito ne daga kasashen Nijar da Sudan da Kamaru da kuma jihohin Legos da Katsina da Yobe da Adamawa da Kano da Borno da kuma Jigawa.

Ya ce asirin masu bikin ya tonu ne a daidai lokacin da suke tsakiyar shirye-shiryen bikin a kauyan na Kadume, wanda bai wuce nisan kilomita uku ba daga cikin garin Jahun.

Ya ce hakimin kauyen ne ya sanar da dakarun na Hisba irin halin da ake ciki, inda suka tarwatsa gungun ’yan daudun da karuwan da suka sauka a kauyan, domin halartar bikin.

Ya kara da cewar amma ba su kama kowa ba, domin su burinsu su hana aikata barna. Ya kuma shawarci dagatai da hakimai da sauran masu unguwa da kuma jama’ar gari a duk inda suke da su taimaka wajan sanar da hukumar Hisba duk wata maboyar bata gari da duk inda ake aikata fasadi, domin ganin an dakile shi.