✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Italiya ba za ta je gasar kofin duniya ba karo na farko a shekara 60

Kasar Italiya ba za ta halarci gasar cin kofin duniya ba wanda zai gudana a kasar Rasha. Wannan ne karon na farko da kasar ba…

Kasar Italiya ba za ta halarci gasar cin kofin duniya ba wanda zai gudana a kasar Rasha.

Wannan ne karon na farko da kasar ba za ta halarci gasar ba a cikin shekaru 60. Kuma kasar ta lashe gasar sau hudu a tarihi.

A wasan karshe, Italiya ta tashi kunnen doki da kasar Sweden a wasa na biyu da aka buga a filin wasan Sansiro da ke kasar Italiya, bayan Sweden ta doke ta da ci daya mai ban haushi a karon farko.

Wannan lamarin ya sanya mai tsaron gidan Italiya na tsawon lokaci, Gianlungi Buffon da Andrea Barzagli da Daniele De Rossi suka sanar da cewa sun yi ritaya daga buga wa kasar kwallo.