✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Jaridar Beijin Times ta yi batanci ga kamfanin ruwa na Nongfu sau 76’

daya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa ruwan kwalba na kasar Sin, Nongfu da ke birnin Hangzhou, babban birnin Gundumar Zhejiang ya aike da korafi ga…

daya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa ruwan kwalba na kasar Sin, Nongfu da ke birnin Hangzhou, babban birnin Gundumar Zhejiang ya aike da korafi ga Hukumar Kula da kafafen yada labarai da gidajen Rediyo da shirya fina-finai da gidajen talabijin, kan yadda jaridar Beijin Times ta buga masa labaran batanci har 76.

“The Beijin Times ta buga labaran bata suna har 76 a kan ruwan kwalba na Nongfu a tsakanin 10 ga watan Afrilu zuwa 7 gaMayun bana. Wannan al’amari ne da ba a cika samunsa a tarihin kasar Sin ba, inda kafar yada labarai za ta yi ta yin batanci a kan kamfani daya,” a cewar korafin kamfanin, kamar yadda aka baza a shafin yanar sadarwarsu na Sina Weibo, a ranar Litinin din da ta wuce.
Nongfu ya ragargajin jaridar Beijin Times kan yadda ta ki saurara musu har sau tsawon kwanaki 26, a tsakanin lokutan da ta yi ta bayar da rahotanni batanci, inda ta yi nuni da cewa ruwan famfo ya fi Nongfu tsafta. Kuma ta yi karya samun bayanai daga ma’aikatar lafiya ta kasa da ta gundumar da ke nuni da cewa rahotanninta na da hujja, kamar yadda takardar korafin kamfanin ta nuna.
Rikicin jaridar da Kamfanin Nongfu ya samo asali ne a ranar 10 ga Afrilun bana, inda rahotannin jaridar suka zargi Nongfu da bin ka’idar sarrafa ruwan kwalba na gundumarsa, maimakon na kasa baki daya, al’amarin da shugaban Kamfanin, Zhong Shanshin ya karyata, da cewa, suna amfani da dokokin sarrafa ruwa na gundumarsu da kuma na kasa baki daya.
A halin yanzu Kamfanin ya kai kara a kotun Beijin, inda yake bukatar diyyar Yuan miliyan 60 (Daidai da Dala miliyan tara da dubu 700), kan batancin da jaridar ta yi masa. Sai dai abin da ba tantance ba, har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoto, shi ne, ko kotu ta karbi wannan kara.
Tuni hukumar kula da kafafen yada labarai da shirya fina-finai ta gargadi kafafen yada labarai da su shiga taitayinsu, musamman in sun yi la’akari da rigimar wannan jarida da kamfanin Nongfu. Kuma kasar Sin ta himmatu yaki da cin hanci da rashawa.