✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Borno ta kafa kwamitin duba yiwuwar bude makarantu

Gwamnatin Jihar Borno ta kafa kwamitin mutum 13 da zai duba yiwuwar bude makarantun gwamnati da suka kasance a rufe kusan shekara biyu da suka…

Gwamnatin Jihar Borno ta kafa kwamitin mutum 13 da zai duba yiwuwar bude makarantun gwamnati da suka kasance a rufe kusan shekara biyu da suka gabata, sakamakon ayyukan ’yan ta’addan Boko Haram, lamarin da ya jawo jibge ’yan gudun hijirar da suka fito daga kananan hukumomi 20 da ke jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya kaddamar da kwamitin  a madadin Gwamnan jihar, kuma ya ce, “Lura da yadda sha’anin ilimi ya tabarbare a wannan jiha tamu sakamakon
tabarbarewar tsaro da jibge ’yan gudun hijira a akasarin makarantu ya sa aka rufe su, don haka a yanzu mun fahimci cewa ci gaba da rufe makarantun zai ci gaba da haifar da mummunar koma baya ga harkar ilimi a jihar don haka muke ganin ya kamata mu duba yiwuwar bude makarantun don amfanin yaranmu.”
Ya ce an kaddamar da kwamitin mai wakilai 13 da zai duba yadda za a samar wa ’yan gudun hijira matsugunai na dindindin a wasu wurare na daban.
Shugaban Kwamitin Alhaji Gambo Gubio ya ce za su yi iya kokarinsu wajen tallafa wa gwamnati da shawarwari kan yadda za a samar wa ’yan gudun hijirar matsugunai na dindindin, ta yadda za a samu damar bude makarantun da ke cikin garin Maiduguri. Ya ce kasancewar harkar ilimi ta samu koma baya a ’yan shekarun dole su mike tsaye wajen dawo da martabar ilimi a jihar.
Wani daga cikin iyayen yaran, Malam Modu Mala, ya bayyana wa Aminiya farin cikinsa dangane da batun bude makarantun.
Ya ce “Na yi murna da farin ciki da yunkurin bude makarantun domin ’ya’yanmu sun zauna na shekara biyu suna zaman gida babu karatu.
Wani dalibi a wata makarantar firamare mai suna Babagana Ali, ya bayyana wa wakilinmu farin cikinsa dangane da batun bude makarantun inda ya ce, ya ji dadi da za su koma makaranta su ci gaba da karatu.