✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohin Arewa maso Gabas sun fi fama da cutar koda – Likita

Babban Likitan Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Nguru a Jihar Yobe DoktaAbubakar Musa ya ce jihohin Arewa maso Gabas da suka hada…

Babban Likitan Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Nguru a Jihar Yobe Dokta
Abubakar Musa ya ce jihohin Arewa maso Gabas da suka hada da Yobe da Borno da Bauchi da Gombe da Adamawa da Taraba ne kan gaba wajen masu fama da cutar koda.
Dokta Abubakar Musa ya bayyana haka ne a tattauwarsa da Aminiya a garin Nguru, inda ya ce kullum suna samun majinyatan da ke fama da cutar koda da ke taruruwa don ganin likita musamman wadanda ke matakin farko da na biyu na wannan cuta.
Shugaban Cibiyar Kiwon Lafiyar ya ce, akasarin mutanen da suke zuwa ganin likita kan wannan matsala a manyan asibitoci da ke Maiduguri da Kano sun fito ne daga yankin Arewa maso Gabas ne musamman Jihar Yobe, kuma a Yobe ma daga kananan hukumomin Jakusko da Bade da Karasuwa da Nguru.
“Babbar matsalar ita ce har yanzu babu wata madogara kan abin da haddasa cutar ballantana a san yadda za a shawo kanta, binciken kwakwaf ne zai nuna hakan,” inji shi.
Dokta Musa ya ce, koda yake a kwanan baya wata tawagar kwararru kan fannin cutar koda sun je Damaturu don bin diddigin abubuwan da suke haddasa kamuwa da cutar, amma abin ya ci tura, saboda haka akwai bukatar da gwamnatin Jihar Yobe ta ba da himma kan nemo hanoyin magance wannan lamari tare da gayyato masana don ganin an gudanar da bincike sosai kan abubuwan da suke haifar da karuwar masu dauke da cutar koda a yankin wadda take haifar da yawan asarar rayukar jama’a.
Ya ce, babbar matsalar da masu dauke da cutar koda ke fuskanta ita ce tsadar magani da kuma dawainiyar je-ka-ka-dawo, inda ya ce idan har ya kai ga sai an yi wa mai cutar canjin jini abin yana da tsada, “Domin akalla a kowane wata mai ciwon koda sai ya tanadi kusan Naira dubu100 domin wannan dawainiya,” inji likitan.
Dokta Musa ya ce ba wannan ne matakin waraka daga ciwon ba, “saboda ba kamar ni ko kai ba, da idan muna da lafiya, kodarmu za ta iya tace abubuwan da muka ci, mai cutar sai na’ura ce za ta yi masa wannan aiki kuma kowane mako akalla a yi wankin jini sau biyu da za a biya akalla Naira dubu 15, ka ga a wata guda kudin zai kai kiminin Naira dubu 120 ke nan ko sama da haka,” inji shi.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dubi muhimman matsalolin da suke addabar cibiyarsa domin magance su musamman karancin dakunan kwantar da marasa lafiya da makamantansu.