✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kananan yara 5 sun rasu a hannun ’yan bindiga a Kaduna

Kananan yara biyar daga cikin mutum 17 da ’yan bindiga suka sace a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna sun rasu a hannun ’yan ta'addar

Kananan yara biyar daga cikin mutum 17 da ’yan bindiga suka yi gakrwa da su a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna sun rasu a hannun ’yan ta’addar.

Kimanin wata guda ke nan da ’yan bindigar suka kai hari a kauyukan Anguwar Ldalele da Unguwar Bawa da ke Gundumar Randagi suka yi awon gaba da mutanen, ciki har da mata masu shayarwa da yaran nasu.

Aminiya ta gano cewa masu garkuwar sun nemi kudin fandas Naira miliyan 19 kuma n ba su, amma sai suka sako mutum hudu suka bukaci a karo musu kudin fansar.

Shehu Randagi, wani shugaban matasa a Randagi, ya ce ’yan bindigar ne suka kira su cewa kananan yara biyar sun rasu saboda rashin lafiyar da ta sa iyayensu ba sa iya shayar da su.

Ya bayyana tashin hankalin da al’ummar kauyukan suke ciki na rashin abin da za su biya kudin fansar da ’yan bindigar ke nema, domin sai da suka sayar duk abin da suka mallaka kafin su iya biyan kudin fansar farko.

Shehu ya ci gaba da cewa a daren Talata kuma ’yan bindiga suka kai  hari a kauyen Unguwar Algaita da ke makwabtaka da su, suka sace mutane 12, ciki har da matan aure.

Amma ya yaba bisa yadda sojoji suka gudanar da aiki a yankin, inda suka kashe ’yan bindiga da dama a Kasuwar Doka da ke kan babbar hanyar Funtuwa zuwa Birnin Gwari.

Don haka ya bukaci sojojin da su ci gaba da zama a kauyen zuwa akalla mako biyu masu zuwa domin hana bata-garin dawowa.

Zuwa yanzu dai babu wani bayani daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna kan lamarin, kuma wakilinmu ya kira kakakin rundunaar, ASP Mansir Hassan, amma wayarsa ta ki shiga.