✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kawancen ’Yan kato da gora da sojojin Najeriya

  Kamar yadda aka ba da shawarar cewa ya kamata a amince da ’yan kato da gora (Cibilian JTF) su shiga cikin sojoji domin tallafa…

 

Kamar yadda aka ba da shawarar cewa ya kamata a amince da ’yan kato da gora (Cibilian JTF) su shiga cikin sojoji domin tallafa musu wajen yaki da ’yan Boko Haram a sassan Arewa maso gabas, Gwamnatin Tarayya ta amince da haka, wanda dalili ke nan ma ya sa ta amince da kafa kwamitin da zai tsara yadda kawancen zai kasance, a karkashin shugabancin Babban Kwamandan Askarawa, Chif Eya Mashal Aled Badeh. Babban aikin kwamitin shi ne, ya tsara yadda za a tsince da tantance irin wadannan ’yan kato da gora da suka bayyana a yankunan Jihar Borno da sauran jihohin da ta’annatin ’yan Boko Haram ya ta’azzara. Haka kuma za a ga yadda za a koya musu da’a da ka’idojin gudanar da irin wannan aiki na dakile aika-aikar ’yan Boko Haram, domin samun gamsasshiyar nasara.
Kwamitin dai yana da kunshiyar wakilcin jami’ai biyu-biyu daga sassan hukumomin tsaron Najeriya daban-daban, zai gano da tantance irin kungiyoyin ’yan kato da gora da ake da su a jihohin da ke karkashin Dokar-ta-baci, wato Borno da Yobe da Adamawa, sannan ya gano irin salon da suke bi wajen tafiyar da ayyukansu. Haka kuma kwamitin zai ba da shawarar wace hukuma ce, baya ga ta soja ta dace ta kula da dawainiyar ’yan kato da gorar. Wanda idan aka samu haka, zai ba dakarun soja su maida hankali da karfinsu wajen tunkarar ’yan ta’addan Boko Haram. Domin kuwa tun da farko, ’yan kato da gora sun tallafa wa sojoji sosai wajen kokarin dakile ta’addanci, musamman ma wajen tona asiri da gano ’yan Boko Haram da mabuyarsu.
’Yan kato da gora sun samu yabo sosai, musamman ma kokarin da suka yi na korar ’yan Boko Haram daga birane, suka gudu zuwa tsaunuka da dazuzzuka. Sai dai su ma ’yan kato da gorar sun jigata, inda ’yan Boko Haram suka rika hakonsu, har ma suka kashe wasu da dama daga cikinsu a ’yan shekarun da ta’annatin nan ke gudana. An ba kwamitin nan damar ya gano yadda za a tsara su zuwa kungiya mai da’a da tasirin yaki da ’yan ta’adda.
Kamar yadda aka tsara cewa za a dauki kimanin mutum 10,000 daga cikin ’yan kato da gora domin saka su yin aikin da ya yi kama da na soja, duk kuwa da cewa su ba sojoji ba ne, akwai hadari cikin al’amarin. Na farko dai, ba su da kwarewa ta fannin aikin soja kuma ba su da makamai na zamani da ya cancanci irin wannan aiki. Haka kuma, ana kallon wasu daga cikin ayyukan da suke yi a matsayin take hakkin dan Adam. Kodayake dai ana ganin cewa idan aka samu nasarar saka su cikin wadannan tsarin, za su samu da’a da tarbiyyar tafiyar da ayyukansu yadda ya dace, wajen yaki da ta’addanci.
Wani abin dubawa daga kwamitin nan shi ne, lallai ne su ba da muhimmanci sosai wajen tantance ’yan kato da korar, domin daukar wadanda suka dace, ba karkatattu masu halayen banza da gurbatattar tarbiyya ba.
Babu ko shakka, ’yan kato da gora sun nuna jaruntaka da himma wajen yaki da ta’addanci, don haka abu ne mai muhimmanci a koya musu aikin sosai yadda za su samu kwarewa takwarai, sannan kuma a sama masu makaman da suka dace da su. Kasancewar a can baya sun taimaka, lallai iliminsu na sanin sirrin ’yan ta’addar nan zai taimaka wa sojojin Najeriya. Haka kuma lallai ne sojojin za su samu tallafi idan suka samu agajin karin mutane, musamman ma wadanda aka koyar kuma aka ba su makamai nakwarai.
Ya kamaka kuma hukuma ta fahimta da cewa za a iya dakile ta’addancin Boko Haram ne kawai ta hanyar karfin soja da kuma hikimomin mulki. Don haka ya dace hukumomin soja su yi tunani mai zurfi, su tanadi yadda za su tafiyar da ’yan kato da gora, idan sun gama aikinsu, wato idan an gama dakile ’yan Boko Haram. Ya dace hukuma ta san yadda za ta raba su da makamai, ta shirya musu bitar wayar da kai, bayan sun gama aikin tallafa wa soja, yadda za su koyi zama da sauran al’umma. Idan an yi musu haka, wannan zai sanya su zama al’umma nagari, yadda su kansu ba za su zama wasu kangararrun dakaru ba kuma ba za su fada hannun bata-garin ’yan siyasa ba a matsayin ’yan banga
Haka kuma, ganin cewa ba dukkan ’yan kato da gorar ne za su samu shiga cikin aikin tallafa wa sojojin ba, to ya kamata gwamnati ta yi tunanin sama wa sauran da za su rage ayyukan yi da koya musu sana’o’in dogaro da kai. Yin haka zai sanya a kauce wa samar da wata matsala mai girma, a yayin da aka dakile wata.