✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Arewa Elite Magazine za ta horar da matasa da mata sana’o’i domin dogaro da kai

kungiyar Arewa Elite Magazine karkashin jagorancin Malam Tijjani Ibrahim tare da hadin gwiwar Majalisar Dattawan Arewa karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ta shirya tsaf domin…

kungiyar Arewa Elite Magazine karkashin jagorancin Malam Tijjani Ibrahim tare da hadin gwiwar Majalisar Dattawan Arewa karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ta shirya tsaf domin gudanar da horo na musamman ga matasa da mata hanyoyin da za su yi dogara da kansu a Kwalejin Barewa da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Taron horarwar, an yi sanya masa taken: Farfarfado da al’adunmu, ilimin kirkira, da samar da hanyoyin rage rashin aikin yi a Arewacin kasa da kuma wayar da kan Matasa da ‘yan mata domin dogaro da kansu a kan sana’o’i da kuma horarwa na musamman  akan harkan shugabanci ta yadda za a samu shuwagabanni nagari a nan gaba. 

Da yake zantawa da wakilin Aminiya a kan dalilin da ya sa suka bude wannan kungiyar da kuma dalilin da ya sa za su shirya wannan horo, Shugaban kungiyar Elite Mazagine, Malam Tijjani Ibrahim cewa ya yi, “Asali mun bude wannan kungiya ce domin wayar da kan mutanen Arewa a kan shugabanci, al’adu da sana’o’in hannu. Muna ba bangaren koyon sana’a fiffiko sosai domin a kullum burinmu shi ne matasa da mata su zama masu dogaro da kansu, domin hakan ne kawai zai kawo mana zama lafiya.

“Dubi da muhimmanci dogaro da kai ne ya sa muka shirya domin gudanar da taron bayar da horo na musamman ga matasa ‘yan uwana da mata hanyoyin da za su dogara da kansu.

“Wannan ne ya sa muka tattauna da Shugaban Majalisar Dattawan Arewa, Magajin Rafin Zazzau, Farfesa Ango Abdullahi kan yadda za mu taimakawa matasa da mata hanyoyin da za su rika dogaro da kansu. Sannan muka shirya hadaka da majalisar ta su domin gudanar da wannan horo, wanda zai gudana a Kwalejin Barewa a ranar 27 ga wannan wata da muke ciki. Sannan kuma wannan taron zai zama somin tabin harkokin wannan kungiya, domin mun kafa ta ne da nufin samar da cigaba da taimakon al’umma, musamman matasa da mata,” in ji Tijjani Ibrahim.

Sannan ya kara da cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan irin wannan a nan gaba da kuma yin rubuce-rubuce masu muhimmanci domin wayar da kan al’umma.