✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kwato Damboa: ’Yan Boko Haram sun jefa Kudancin Yobe cikin damuwa

Ga dukan alamu tsugunne ba ta kare ba ga al’ummomin da ke Kudancin Jihar Yobe, musamman na kananan hukumomin Gujba da Gulani da Fune da…

Ga dukan alamu tsugunne ba ta kare ba ga al’ummomin da ke Kudancin Jihar Yobe, musamman na kananan hukumomin Gujba da Gulani da Fune da Fika da ke fama da hare-haren ’yan Boko Haram sakamakon kauratowar da suke yi zuwa yankunan saboda tarwatsa su da sojoji suka yi daga garin Damboa a Jihar Borno.
Majiyoyi a Kudancin Yobe sun bayyana wa Aminiya cewa, duk da kaurace wa yankunan da al’ummomi ke yi, sai ga shi ’yan kungiyar Boko Haram da suka kori galibin jama’ar yankin na kokarin mayar da wurin tungarsu bayan korarsu daga Damboa da sojoji suka yi.
Wani makeri dan asalin Buni-Yadi da ya nemi a sakaya sunansa kuma ke gudun hijira a garin Damaturu ya bayyana wa Aminiya cewar, a ranar Jumu’a ya yi kokarin tafiya garinsu don debo wasu kayansa, sai ya tarar da wasu ’yan Boko Haram sanye da kakin soja na shawagi a garin, nan da nan ya dawo ba tare da ya yi abin da ya kai shi ba.
Ya ce wani abokinsa da ya tarar a garin ya ce duk inda aka zaga a yankin nasu matasan za a tarar dauke da bindigogi sun kafa shingaye suna tare mutane don biyan wasu bukatunsu.
Wani direban mota da ya biyo hanyar Bara, hedikwatar karamar Hukumar Gulani da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa tunda ya fito yake haduwa da ’yan bindigar a hanya, amma ba su tare shi ba.
kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Kakakin Rundunar JTF a jihar, Kyaftin Eli Lazarus kan wannan lamari da matakin da za su dauka ya ci tura.