✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lyon ta bai wa Juventus mamaki a Faransa

Kungiyar kwallon kafa ta Lyon ta doke Juventus da ci daya mai ban haushi 1-0 a wasan farko zagaye na biyu a gasar Champions League.…

Kungiyar kwallon kafa ta Lyon ta doke Juventus da ci daya mai ban haushi 1-0 a wasan farko zagaye na biyu a gasar Champions League.

Dan wasan tsakiya na Lyon mai suna Lucas Tousart,ne ya jefa kwallo a ragar Juventus tun a minti na 31 kuma ta rike kungiyar har aka tashi a gasar Zakarun Turai da aka buga daren ranagr Laraba.

Juventus dai na daya daga cikin kungiyoyi da ake sa ran zasu iya cin gasar a bana, sai dai wasan na jiya ya kawo shakku cikin yiwuwar kungiyar ta Italiya zata iya cin gasar duk da sayo manyan ‘yan wasa kamar su: Cristiano Ronaldo, De Light, Rabiot, Ramsey da Higuain.

Hankula za su karkata zuwa wasan da Juventus din zata karbi bakwancin Lyon a filin wasa na Turin a kasar Italiya, inda ake saran za’a barje gumi tsakanin kungiyoyin biyu don samun gurbin wasan kusa dana kusa dana karshe a gasar Zakarun Turai.