✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya baya a fahimci Jam’iyyun PDP da APC

Siyasar Najeriya na tafiya ne tsakanin APC da PDP, haka kuma al’ummar Najeriya sun kasu gida biyu, ko dai masu nuna goyon baya ga PDP…

Siyasar Najeriya na tafiya ne tsakanin APC da PDP, haka kuma al’ummar Najeriya sun kasu gida biyu, ko dai masu nuna goyon baya ga PDP ko kuma APC. Don haka yana da kyau mu fahimci cewa, ita Jam’iyyar siyasa wani dandamali ne da ake takawa a hau don kaiwa ga dare madafun ikon shugabantar al’umma. A bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, babu wani mutum da zai iya zama shugaba a kowanne mataki na wakilci, ko zartarwa sai ya biyo ta kwararon jam’iyyu.
Al’umma kan yi kuskuren fahimtar siysar jam’iyya da ma’anarta. Da dama sukan dauka tilas ne siyasa ta zama gaba tsakanin mutanen da suke jam’iyyu mabambanta. Watakila yau da Buhari zai gayyaci shugaban kasa su ci abincin rana tare su biyu, sai dukansu su zama abin zargi a wajen magoya bayansu.
Ya isa abin misali a ce maka Atiku Abubakar, wanda jigo ne a APC, kuma yake taimaka mata ta kowanne fanni don samun nasararta, amma a ce dansa na cikinsa yana auren diyar Ahmed Adamu Mu’azu, wanda shi ne Shugaban jam’iyyar PDP na kasa baki daya! Jam’iyya ta bambanta su, amma kuma su surikan juna ne. Shin wannan ba zai zama darasi gare mu ba?
Gwamnan Bauchi Isa Yuguda yana ANPP ya auri diyar shugaban kasa marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua. Shin idan siyasar jam’iyya gaba ce, Shugaban kasa zai aura wa dan ANPP ‘yarsa ta cikinsa? Haka fa Tsohon Gwamnan Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi yana ANPP ya auri diyar tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida, wanda jigo ne, kai kusan shi ne babban fulogi a PDP suka zama surikan juna.
Ka koma baya ka ga yadda AbM Mukhtar Mohammed yana ANPP kuma dan-gani kashenin Janar Buhari, amma kuma matarsa da yake aure tana PDP, inda ta yi takarar Sanata, wannan kuma bai kawo komai a cikin auratayyarsu ba, sai karuwar dankon zumunci da soyayya da kaunar juna. A Kwara yanzu Bukola Saraki na APC, kanwarsa uwa daya, uba daya tana PDP, hakan kuma bai haifar da komai a alakar dangantaka tsakaninsu ba, sai zumunci da kaunar juna.
Sai dai mu da muke na can kasa, da muka fi su iya fahimtar siyasa muke zaton cewar dolenmu mu zama abokan gabar juna, matukar jam’iyyunmu sun bambanta, mu dinga jifar juna da miyagun kalmomi da munana kalamai? Ya kamata mu nutsu mu yi hankali musan inda yake mana ciwo. Da PDP da APC dukkan su jam’iyyu ne da babu wadda aka gina manufofinta don fita wa’azin maguzawa, babu wacce aka gina don kare addinin Musulunci ko kare muradun Musulmi.
Yana da kyau mu fahimci cewar mu da muke nuna wa juna adawa maras kyau, mara kan gado saboda bambancin jam’iyya sai mu zama abin dariya a wajen wadanda muke gani su ne shugabanni. Idan mun gamsu tare da juna a wajen taruka suna taya juna murna. Sau nawa muke ganin hotunan Buhari da Obasanjo a taruka suna musabiha suna yi wa juna dariya? Bayan kuma dukkanmu mun san cewar an yi takara tsakanin Obj da Buhari a 2003 da 2007 har aka je kotu dan kwatar hakki? Shin Obasanjo da Buhari ba sa kishinmu ne, suke musabiha da juna a gaban kyamara?
A zaben 2011 da aka yi takara tsakanin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, babu wani abu na nau’in rashin jin dadi da bai faru ba, an yi wa mutane da dama ta’adi da sunan goyon bayan wadannan mutane. Amma a bikin cikar Najeriya shekaru 100 aka nuna Shugaban kasa Jonathan yana rataya wa Buhari lambar girma a wuya dukkansu suna yi wa juna dariya, karshe kuma suka yi musabiha.
Meye Kwankwaso bai yi wa Buhari ba a lokacin zaben 2003? Amma yau da Buhari da Kwankwaso suna cikin jam’iyya daya. Wane irin abu ne bai faru ba tsakanin Bafarawa da Wamako ba, amma sai da suka hada jam’iyya daya, kuma suka yi magana da juna. Duk wadannan jagororin siyasar muna jin mu da muke mabiya mun fisu fahimtar siyasa ne?
Yau ina Najatu Mohammed, ina Buhari? Wace irin magana ce Najatu ba ta gaya wa mutane akan Buhari ba, amma yau sun raba gari da Buhari jam’iyyarta daban ta Buhari daban, ya kamata mu fahimci maganar da ake cewa Siyasa ba ta da tabbataccen masoyi, kuma bata da tabbataccen makiyi.
Ya kamata mu sani cewa idan hankali ya bata, to, hankali ne yake nemo shi. Dukkanmu fatan Allah ya ba mu shugabanni nagari muke yi, kuma kowa yasan ba Mala’iku za’a turo mana ba, kuma ba wani mutum za a sauko mana da shi daga sama ba ya zama shugabanmu, daga cikinmu shugaban zai fito. Tayaya muke fatan samun kyautatuwar rayuwa alhali mu ba mu mutunta kanmu, ba mu mutunta wadanda muke fatan nan gaba su zama shugabanni ba?
Ya zama dole mu fahimci tsantsar gaskiya dangane da siyasar Najeriya da kuma siyasar Jam’iyyar PDP da APC. Babu wata jam’iyya da aka bude kundinta da Bisimillah. Babu kuma wata jam’iyya da ake aiwatar da manufofinta a duk jihar da take Mulki. Da gwamnatin Akwa Ibom da Gwamnatin Yobe ba su da wani bambanci wajen tafiyar da jagoranci, duk abin da Gwamna yake so shi ake aiwatarwa ko ya dace da jam’iyya ko bai dace ba, haka abin yake a ko ina a Najeriya.
Don haka, mu ne za mu ci gaba da kasancewa a wahale, wasu na can a kwance suna amfanuwa da jahilcinmu gidadancinmu na kin fahimtar ma’anar ita kanta rayuwarmu da kuma siyasa da hamayyar siyasa.
Za mu zama azzalumai na gaske idan jam’iyyar siyasa ta zama ita ce ma’aunin mutanen kirki da na banza a wajenmu. Mutum ya yi duk abin da ya ga dama a PDP, amma daga ranar da ya shiga APC sai a yi masa kallon shi tsarkakakke ne. Shi ke nan mun zama gidadawa na karfi da yaji?
Masu mulki sai su handame, su tara, su kuntata ga son kai da wawura. Sai ma ka ga wata tsana ko kiyayya ta shiga tsakanin su da al’umma. Ba tausayi, ba hange ba tuna makoma ba waiwaye da daukar izina daga darassin rayuwar su ta baya ko rayuwar wani da suka sani.
Wadannan al’amura da ke faruwa ba za su zama izna a garemu ba? Sai mu koma jifar juna da miyagun kalmomi da kazafi da karairayi kawai, saboda bambancin ra’ayin siyasar jam’iyya! Wace irin al’umma ce mu? Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimceta, Ka ba mu ikon binta ka nuna mana karya mu fahimceta ka ba mu ikon kauce mata.