✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makami mai linzami da koriya ta Arewa ta kaddamar ya harzuka Japan

Firayiministan kasar Japan shinzo Abe ya ce kasar na fuskantar “mummunar barazana” bayan da kasar Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami yak eta…

Firayiministan kasar Japan shinzo Abe ya ce kasar na fuskantar “mummunar barazana” bayan da kasar Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami yak eta sararin sam aniyar Arewacin  Japan. Wannan al’amari ya harzuka Japan, har sojojinta sun fara atisaye don kare kasarsu daga kowane irin farmaki.

Makamin da Koriya ta Arewa ta kaddamar a babban birnin kasar Pyongyang, ya cilla sama, inda ya ci nisan kilomita dubu biyu da 700, ya kuma kara karade wata kilomita 550 a sama.

Sararin samaniyar Arewacin Japan daf da tsibirin Hokkaido, inda makamin ya farfashe ya fada cikin teku kimanin kilomita dubu da 180 a gabashin Japan..

Tuni kasar ta gargadi mazauna Arewacin kan yadda za su tarairayi al’amarin, inda aka yi yekuwar samun mafaka.

A karkashin jagorancin matashin shugaban kasar Koriya ta Kudu Kimn  Jong-un an yi gwajin makamani masu linzami da suka keta saman  kasar Japan.