✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamar jami’a ta ajiye aiki ta shiga kungiyar IS

Wata malamar Jami’a da ke koyar da Hukunce-Hukuncen Shari’a da Tsarin Tsimi da Tanadi na addinin Musulunci a Jami’ar birnin Dammamm da ke kasar Saudiyya,…

Wata malamar Jami’a da ke koyar da Hukunce-Hukuncen Shari’a da Tsarin Tsimi da Tanadi na addinin Musulunci a Jami’ar birnin Dammamm da ke kasar Saudiyya, ta ajiye aikinta domin shiga kungiyar Daular Musulunci ta (IS) kamar yadda ta bayyana wa dalibanta kwanakin baya. 

Matar mai suna Eman Mustapha al-Bugga wadda ’yar asalin kasar Siriya ce, ta kwashe shekaru masu yawa tana koyar a jami’ar. Kamar yadda kafar yada labarai ta Arab News ta bayyana malamar ta rubuta a shafinta na Twitter cewa ta bar aikinta ne duk da rayuwar jindadin da take ciki da kuma albashin da take karba mai tsoka saboda koyi da marigayi Osama Bin Laden. Kuma ta bayyana biyayyarta ga Shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi.
Wadanda suka yi wa malamar farin sani sun ce an santa da yin kira kan Jihadi a wa’azinta kuma ta kan bayyana ra’ayoyinta a fili kan kaifin kishin addini a shafinta na Facebook da Twitter.
Hukumar jami’ar ta tabbatar da ajiye aikinta. Kodayake mai magana da yawun jami’ar Ibrahim al-Khaledi ya ce ta yi hakan ne saboda dalilan kashin kanta. Al- Khaledi tun da farko ya yi kokarin nuna wa duniya cewa daliban makarantar ba sa tasirantuwa da hukunce-hukuncen da suka ci karo da shari’a da kuma sunnar Manzon Allah (SAW). An ruwaito cewa malamar ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: “Allah ya albarkaci kungiyar IS, wadda na sadaukar da kaina gareta,” inji ta.
Daga nan sai ta yi bayani ga dalibanta dalilin da ya sa ta bar su, inda ta ce: “Na guje muku ne saboda ina neman mafakar da za ta ba ni damar fadin gaskiya daga can.”
Ta ci gaba da cewa: “Daular Musulunci na bukatar shahidai, wadanda suke masana kimiyya da suka guje wa jindadin duniya don yi wa Musulmai shari’a. Mutumin da nake koyi da shi shi ne Osama bin Laden, wanda yake rayuwa a kogo, ya bar biliyoyin kudinsa don ya yi kira zuwa Jihadi. Na bar albashina mai tsoka don na shiga cikin Musulmai masu dauke da makamai da suke yakar mulkin kama karya.” inji ta.