✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manjo Al-Mustapha ya raba wa mutanen Kudancin Kaduna tallafi

Dogarar marigayin Shugaba Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ziyarci Kudancin Jihar Kaduna inda ya raba wa mutanen kauyen Attakar da ’yan bidiga suka kora…

Dogarar marigayin Shugaba Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ziyarci Kudancin Jihar Kaduna inda ya raba wa mutanen kauyen Attakar da ’yan bidiga suka kora da daga gidajensu tallafi, inda ya ce, nan ba da dadewa ba zai taimaka wajen kawo karshen rikice-rikicen da ke aukuwa a yankin.
Manjo Al-Mustapha ya danganta kashe-kashen da ke faruwa a yankin da rikicin siyasa na shekarar 2011 inda ya yi kira ga mutanen yankin su yafe wa juna domin a samu zaman lafiya a yankin.
“Yaranmu ba za su ji dadi ba, idan muka bari wannan kiyayya ta ci gaba a tsakaninmu. Bai kamata a ce muna rigima ba, kamata ya yi mu rika mutunta juna. Ina rokon duk wanda aka kashe wa dan uwa ya yafe dole ne Musulmi da Kirista su yafe wa junansu,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Ba za mu taba yarda da kashe-kashen da ke aukuwa a Kudancin Jihar Kaduna ba. Domin iyayenmu sun dade suna zaune da juna lafiya. Manufar zuwata nan ita ce domin samar da zaman lafiya. Rikicin shekarar 2011 da kuma na kan iyakar jihohin Filato da Kaduna na daga dalilan da ke kawo rikici a Kudancin jihar nan. Don haka zan yi iya kokarina wajen ganin an kawo karshen rikicin kan iyakar Filato da Kaduna.”  Ya sha alwashin gayyatar masu rigimar zuwa Abuja domin a tattauna yadda za a magance wannan rikici saboda abin da ke faruwa a yankin abin damuwa ne matuka.
Majon Al-Mustapha ya shawarci mutanen yankin su kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin kunyata mugayen da da ke shiga tsakaninsu. Ya ziyarci fadojin wasu daga cikin sarakunan yankin kafin shi da tawagarsa su bar yankin.