✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marubuci Yusuf Dingyadi ya samu sarautar ‘Magayaki’

A gobe Asabar ne Majalisar Garkuwan Sakkwato za ta gudaar da bikin nadin kwararren dan jarida kuma marubuci, Malam Yusuf Abubakar Dingyadi sarautar ‘Magayakin Garkuwan…

Magayakin Garkuwan Sakkwato, Malam Yusuf Abubakar DingyadiA gobe Asabar ne Majalisar Garkuwan Sakkwato za ta gudaar da bikin nadin kwararren dan jarida kuma marubuci, Malam Yusuf Abubakar Dingyadi sarautar ‘Magayakin Garkuwan Sakkwato,’ Alhaji Attahiru Bafarawa.
Kamar yadda Aminiya ta kalato, Garkuwan Sakkwato, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma jigo a jam’iyyar hada-ka ta APC, ya amince da nadin nasa ne saboda yabawa da irin namijin kokarinsa wajen kare martabarsa da ta sarautarsa da kuma masarautar Sakkwato gaba daya.
Sabon Magayakin Garkuwan na Sakkwato, Malam Yusuf Dingyadi, an haife shi ne a garin Kwalfa (Tulluwa) da ke tsohuwar gundumar Dingyadi, karamar Hukumar Bodinga, Jihar Sakkwato, kusan shekaru 43 da suka gabata. Ya yi dukkan karatunsa na addini da na zamani a garin Sakkwato. Ya fara aikin jarida kusan farkon shekarar 1990. Jaridar farko wadda ya fara aiki da ita a lokacin, ita ce Nasiha, ’yar uwar The Reporter  ta Turanci, wadda kamfanin buga jaridun Nation House da ke Kaduna ya rika wallafawa. Daga lokacin zuwa yau, ya yi aiki da kafofin watsa labarai daban-daban, a matsayin wakili, mai aika rahoto da kuma jami’in gudanarwa. Ya taba yin aiki da Sashen Hausa na BBC Landan, inda ya zama wakilinsu a Jihar Sakkwato da kewaye.
A wata tattaunawa ta musamman da Aminiya ta yi da Magayakin Garkuwa, Malam Yusuf ya bayyana farin cikinsa da wannan sarauta da Garkuwan Sakkwato ya ba shi. “Wannan sarauta ta kara tabbatar mani da gamsuwa da yadda nake gudanar da aikina na fadakar da al’umma tare da kare martabar al’ummar Jihar Sakkwato da kasa baki daya. Babu shakka za ta kara mani kaimi wajen ci gaba da aikina kamar yadda na saba.”
Nadin, wanda za a gudanar da misalin karfe biyu na rana a fadar Garkuwan Sakkwato, Attahiru Bafarawa da ke Sakkwato, zai samu halartar dinbin jama’a masu rike da sarautun ngargajiya da ’yan siyasa da kuma ’yan jarida daga kafafen watsa labaru daban-daban da ke ciki da wajen Najeriya.