✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maulidi da Kirsimeti: Shugabanni sun taya al’umma murna

A jiya da yau ne aka fara bukukuwan Maulidi da Kirsimeti na bana, inda al’ummar Musulmi da Kirista ke murnar zagayowar ranakun haihuwar Annabi Muhammadu…

A jiya da yau ne aka fara bukukuwan Maulidi da Kirsimeti na bana, inda al’ummar Musulmi da Kirista ke murnar zagayowar ranakun haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) da  Annabi Isa (AS) a sassa daban-daban na kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakonsa na Mauludi ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, (SAW).
Kakakin Shugaban kasa, Mista Femi Adesina ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai. Ya ce Shugaba Buhari ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi amfani da wannan lokaci wajen nazarin koyarwar Manzon Allah, wanda ya rayu cikin tawali’u da jinkai da bautar Allah tare da yi wa al’umma hidima.
Shugaban ya ce, a yayin da al’ummar Musulmin Najeriya da na sauran duniya ke bikin tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah, ya nemi su maida hankali wajen aiki da koyarwar Alkur’ani wajen tafiyar da rayuwarsu da ta sauran al’umma da suke mu’amalar yau da kullum tare.
A sakon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, kira ya yi ga ’yan Najeriya su zauna lafiya da juna, sannan su dauki bikin Maulidin kamar wata dama ce ta sabunta akidoji masu kyau a Najeriya.
Jawabin Gwamnan ya zo ne ta bakin Kakakinsa Malam Imam Imam.
Gwamnan ya roki al’umma da su yi koyi da Manzon Allah Muhammad (SAW) kuma su yi kokarin zaman lafiya da kwanciyar hankali da abokan zama. “Yadda haihuwar Manzon Allah ta samar da canji mai alfanu ga al’umma, ina kira ga al’umma su yi amfani da wannan biki na maulidi wajen sabunta kudurorinsu yadda za a samu canji mai kyau a kasar nan,” inji shi.
“Na yi amanna cewa za mu samu nasara wajen bunkasa kasa mai dauke da hadin kai da yalwar arziki matukar al’ummarmu ta yi koyi da halayen Manzon Allah na jinkai, aminci, juriya, gaskiya, amana, adalci da zaman lafiya da juna.”
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, baya ga murna da ya taya al’ummar Musulmi, ya kuma taya al’ummar Kirista murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa (AS), wacce ta yi daidai da yau Juma’a.
Ya ce haihuwar Annabi Isa (AS) ta nuna yadda Allah ke kaunar al’umma, domin a zauna cikin mutunci da zaman lafiya da juna.
Gwamnan Jihar Oyo, Isiak Ajimobi, ya roki al’ummar Musulmi da Kirista na kasar nan su zauna lafiya da juna, musamman ganin yadda bukukuwan Maulidi da Kirsimeti suka zo kusan lokaci guda.