✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministan tsaro ya hori daliban makarantar sojoji kan biyayya

Ministan Tsaro Janar Aliyu Gusau (mai murabus) ya hori daliban makarantar sakandaren sojoji da ke Zariya su zamo masu biyayya da kyawawan dabi’u domin su…

Ministan Tsaro Janar Aliyu Gusau (mai murabus) ya hori daliban makarantar sakandaren sojoji da ke Zariya su zamo masu biyayya da kyawawan dabi’u domin su yi nasara a aikin soja.
Janar gusau ya furta haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin bikin cika shekara 60 da kafa makarantar wadda aka gudanar a harabarta da ke Zariya.
Ministan ya ce idan dalibai suka zama masu kyakkyawar dabi’a ne za su dora kasar nan a kan turba tagari.
Janar Aliyu Gusau ya ce makarantar ta dade tana yaye mashahuran mutane da suka ba da gudunmawarsu ga ci gaban kasa a fannoni daban-daban.
Ministan ya yaba wa mutanen Zariya dangane da hadin kan da suke ba jami’an tsaro masamman sojoji wanda hakan ya haifar da zaman lafiya da ci gaban kasa.
“Kasancewan haka ne ya sa Zariya ta mallaki cibiyoyin karantarwa kamar Jami’ar Ahmadu Bello da makarantar koyon tukin jiragen sama da makarantar kuratan sojoji mafi girma a kasar nan,” inji shi.
Wakilinmu ya rawaito cewa Ministan ya shiga ya ci abinci tare da daliban makarantar domin nuna musu soyayya.
A karshe an gudanar da faretin girmamawa ga manyan hafsoshi na yanzu da wadanda suka yi murabus.