✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nagarta Cikin Aminci: Tarihin rayuwar M. D. Yusuf

Wannan littafi na uku ke nan a jere a kan rayuwar tsohon Sufeto-Janar Muhammadu Dikko Yusuf. Na farko shi ne littafin da Mista Mathias Oke…

Wannan littafi na uku ke nan a jere a kan rayuwar tsohon Sufeto-Janar Muhammadu Dikko Yusuf. Na farko shi ne littafin da Mista Mathias Oke Oyouyo ya rubuta, mai suna ‘Beyond the Cop.’ Sai kuma na Ayo Opedukun da ya yi wa lakabi da ‘Aristrcratic Rebel.’

Kowane daga littafan nan biyu, a hakika marubutansa sun bayyanar da kwarewa da gogewarsu a fannin Adabin Ingilishi, don haskaka rayuwar tsohon Sufeto-Janar din. Amma Abubakar Mijinyawa kuma, a nasa littafin, ya kara mirginawa gaba wajen zurfafawa, don fito da wasu sabbin bayanai masu ilimantarwa, nishadantawa da kuma fadakarwa, dangane da rayuwar Muhammadu Dikko Yusuf, don masu karatu su kashe kishin ruwan karatun tarihin rayuwar wasu muhimman mutanen Arewacin Najeriya, a cikin harshen Hausa.
Wadannan bayanai kan rayuwar M.D. Yusuf, kamar yadda Dokta Abubakar Saddik da ya dan lika ta’alikinsa a littafin, ya ce: “Ba wata tababa, wannan littafi yana kunshe ne da tasakokin ilimi masu rai da motsin watayawa a kan kafafunsu…”
Wannan littafi, a zahirin magana, ya bankado dawwamammu kuma zurfafaffun bayanan tarihi na kunne ya girmi kaka; wadanda suka samo tushensu tun ma kafin Jihadin Musuluncin da Shehu Usman danfodiyo ya jagoranta. Sannan kuma ya gangara kan bayanan ababen da suka wakana a tarihi, lokacin mulkin mallakar Turawan Ingilishi a Najeriya da kuma wadanda suka kasance bayan samun ’yancin kan Najeriya. Bugu da kari kuma, littafin ya fayyace filla-filla, bayan tacewa, sannan kuma ya yi sharhi kan wadansu al’amuran da suka jibanci rayuwar wasu muhimman mutanen Jihar Katsina da ma yankin Arewacin Najeriya baki daya.
Kazalika, littafin ya kunshi wasu muhimman bayanai da maudu’ai, wadanda suka jibanci wasu manyan al’umaran da suka shafi al’adu da kuma ci gaban yankin Arewacin Najeriya baki dayansa, tun daga dauri da kuma yadda suka rika samun wasu sauye-sauyen da suka datar da su da zamanin da ake ciki yanzu.
Sai dai kash, wani hanzari ba gudu ba shi ne, cewa littafin ya fito ne a wani lokacin da al’adar karance-karancen littattafan Adabin Hausa don samun bunkasauwar kaifin basira da tunanin jama’ar Hausawa da sauran masu magana da harshen ke fuskantar barazanar dusashewa. Wannan abin takaicin kuma ba ya rasa nasaba da gaskiyar cewa, akasarin matasan yau sun gaza fahimta da kuma lakantar lakanin asirin da ke cikin halayyar karance-karancen littattafai, wajen habakar da hazaka, zalaka da kuma kwarewa da gogewar mutum wajen sarrafa harshe.
In abin a fede biri har jelarsa ne ma, to ana iya cewa, hankulan matasan na fama da cutar kanjamau din da a fannin nazarin kere-kere da kage-kagen zamani, za a ce da shi “halayyar hamburum-hayam” din hadiyar duk wani abin da aka kero aka mika musu, ba tare da la’akari da illolin da ke tattare da hakan ba.
Wannan matsalar ce ta sa jama’a a yau suka zama marasa sha’awar gina wa kansu da kansu al’adar karance-karancen ababan karatu; misalin littattafai, mujallu, jaridu da makamantansu. Amma a daura da haka kuma, suka zama bayin na’urorin nasarar da suka yi wa rayuwa daurin tankila. Sannan kuma ba kasafai wadannan na’urorin ke bayar da wata gudunmowar a zo a gani ba, wajen bunkasa kaifin kwakwalwa da hazakar mutane yayin sarrafa harshe. Batun habbaka ilimi kuma, ture shi gafe ma kawai.
Littafin ‘Nagarta Cikin Aminci,’ idan har mutum zai mallaki kwafinsa, to, zai farfadar da sumammiyar al’adar karance-karancen littattafan Hausa. Idan kuma matacciya ce, to, zai sake rayar da ita cikin kudurar Mai duka, a zukatan makaranta.
Domin marubuta, a zahirin gaskiya su ne kan yi amfani da hikima da basirar da Allah Ya huwace masu, don yin nitso cikin zurfin kogin tarihin mutane, walau a jama’u ko a daidaiku, don dauko sahihan ababe kyawawa da munana, don baje kolinsu ga jama’a. Wannan ne ma abin da ya sa Mijinyawa ya yi wa daya daga cikin Katsinawan Dikko kallon tsaf, wato M.D. Yusuf, don fitar da wasu nagartattun darussan da masu karatun littafinsa za su koya.
“Malaman tarihi da masu binciken ilimin kufai, dukkaninsu sun yi ittifakin cewa birnin Katsinan yau, ya kafu ne sakamakon kafuwar sansanoni da tungayen da wani gungun mafarauta na ’yan kabilar Adawa, a gindin dutsen Durbi-ta-Kusheyi; sannan kuma suka sa wa mazaunan suna Birnin Bugaje, kimanin shekaru 3,500 da suka gabata, sannan kuma ya ci gaba bunkasa har zuwa yanzu. Manyan sana’o’in mutanen, a wancan lokacin kuma, su ne hako tama don yin kirar kayayyakin aikin gon da farauta. Sarki na farko da ya fara sarauta a tsohuwar daular Katsina, daga jerin sarakunan habe, shi ne Bagiri-Jirgo… Amma dai habakuwar sha’anin mulki da sarautar Katsina, ya somo ne daga kan sarautar Sarki Korau (shafi na1 zuwa na 2).”
Har ila yau kuma, marubucin ya janyo hankulan masu karatu kana abin da aka manta, wannan kuma, da ma shi ne asasin da sana’ar rubutu da talifin adabi ya shahara da shi. Idan har mawallafi ya iya farkar da mutane zuwa ga ababen da suka manta da su ko kuma ya karkatar da tunaninsu zuwa ga bai wa wadannan ababen kimar da suka dace da su, walau masu karatu sun ankare da hakan, ko a’a, to fa mwallafin ya cimma muradin da ake nema a sana’ar ke nan. Don haka, da wannan, ana iya cewa littafin ya taka wannan rawar; kasancewar ya fitar da tarihin kafuwar Katsina da sarautarta a fili fayau, ta hanyar tarihin rayuwar daya daga cikin ’ya’yanta kuma a harshen da ya fi kowane karbuwa da kuma yawan masu magana da shi a yankuna Afirka Ta Yamma da wasu muhimman yankunan Afirka Ta Arewa da ta tsakiya; wato harshen Hausa.
A wannan littafin mai dauke da babi tara, daidai gwargwado, an yi sahihantaccen bincike mai zurfi, don tantancewa da kuma kalailaice bayanai na tarihin kunne ya girmi kaka da kuma wadanda aka samo ta hanyar rubutattun bayanai. Saboda haka ana iya cewa marubucin ya kawo sauyi a rubuce-rubuce cikin harshen Hausa na zamanin yau, wadanda galibin manyan jigoginsu soyayya ne,da kuma lamurran da suka shafi zamantakayyar aure da auratayyar; gami da wasu akibobin da ke tattare da su a fannonin siyasa da tattalin arziki. Kazalika kuma ya yi rubutunsa ne a tsohon salon zube irin na hikaya.
Rubuta wannan littafi a harshen gida da kowa ke magana da shi, maimakon harshen gwamnati, wato Ingilishi; duk da hakan, ko shakka babu, zai taimaka wa malamai a manyan makaratun ilimi wajen bincike. Hakazalika kuma a makarantun sakandire, musamman a fannonin ilimin tarihi da nazarin ilimin zamantakewa da kuma gudanar da gwamnati. Domin ya haskako yadda siyasar kasar nan na ta kasance tun kafin zuwan Turawan mulkin mulak’u da kuma yadda ta rika wakana bayan sun kafa mulkinsu da kuma yadda ta sauya salo iri-iri, bayan samun ’yancin kai, musamman ma dai a Arewa da kuma kasa baki daya.
Har ila yau kuma, littafin ya hakaito yadda aka faro aikin ’yan sanda a Nijeriya da kuma irin gudunmowar da M. D. Yusuf, a matsayinsa na Yariman Katsina sannan Sufeto-Janar ya bayar, wajen inganta aikin; hususan ma dai a lokacin da Najeriya ta shiga ciki halin walagigin siyasa.
Misali a nan shi ne, lokacin da aka yi juyin mulkin da bai yi nasara ba ga gwamnatin sojan marigayi Janar Murtala. A lokacin, akasarin manyan jami’an soja ’yan Arewa sun fi son Janar T. Y. danjuma ne ya maye gurbin marigayin, a maimakon Janar Obasanjo. Amma danjuma ya ki amincewa da wannan bukatar, M. D. Yusuf kuma bai yi wata shafanya ba, wajen goyon bayan danjuma kan haka (duba shafi na 177). Wannan ma wani kakkyawan misali ne na kamanta gaskiya da adalicin da aka san M. D. da shi lokacin da yake cikin kayan sarki.
“Duk da cewa shi dan gidan sarauta ne, sannan kuma ga shi babban jami’in ’yan sanda amma an shaide shi da cewa bai taba amfani da matsayinsa ba, don cimma wani muradi na kashin kansa; wadanda suka san shi, farin sani kuma, sun san shi a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana, adala da kuma bayyanar da ruhin ’yan uwantaka a tsakanin wadanda ke kasa da shi a mukami ko ga wadanda ke sama da shi. M. D. Yusuf ne kuma jami’in ’yan sandan da tarihi aikin a Najeriya ya tabbatar da cewa ya fara aikin dan sanda daga mukamin Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda. Dalilin haka kuwa shi ne, gasikya da rikon amana gami da sadaukar da kan da ya rika nunarwa a duk ayyukan da ya yi (duba shafi na 88 zuwa na 89).”
Littafin ya kuma hakaito irin gwagwarmayar da M. D. ya yi da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha, lokacin da Abachan ya so dawwamar da kansa a kan karagar mulkin Najeriya, a matsayin Shugaban kasa na farar hula, bayan ya kwabe kakin soja. A daura da wadannan muhimman bayanai masu ilmantarwa kuma, litafin ba ya rasa ’yan kura-kurai ta fuskar amfani da karbabbe kuma sahihin tahaji’in harshen Hausa. Don haka, akwai bukatar a sake duba shi don tsabtacewa, duk kuwa da ana sa ran kaddamar da shi ne ran 18 ga watan Nuwambar bana; musamman ma dai da yake ana son a yi amfani da kudaden da za a tara lokacin kaddamarwar ne wajen gina wani katafaren dakin karatu na zamani, mai dauke da babban dakin taro irin na zamani a Katsina, da nufin bunkasa Adabin Hausa. Ashe ke nan, bai kamata magini ya ci da tsingaro ba; idan har ana batun bunkasa harshen ne.
Gwantu ya aiko da sharhin nan daga Kaduna, kuma za a iya samunsa ta: [email protected] ko kuma ta 08022519320